Labaran tattalin arzikin Najeriya
Gwamnatin tarayya ta bukaci ‘yan kasuwa su rage farashin kayan abinci yayin da ta tallafa wa manoman Jigawa da kayayyakin noma na Naira biliyan 5.
Mai kudin Afrika, Aliko Dangote ya bayyana kalubalen da ya fuskanta yayin gina matatar mai da ke Legas. Ya ce da ya gaza karasa aikin da ya samu karayar arziki.
Hukumar kididdiga ta kasa watau NBS ta bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya yi gagarumar faɗuwa daga 34% zuwa 24.48% a watan Janairu.
Karamin Ministan tsaro, kuma tsohon gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya bayyana cewa 'yan Arewa su na ganin amfanin mulkin Bola Ahmed Tinubu a fannoni da dama.
Gwamnatin tarayya ta nemi sabon bashin dala miliyan 300 daga Bankin Duniya don inganta kiwon lafiya, NCDC ce za ta aiwatar da shirin a shekarar 2026.
Daya daga cikin sababbin limaman masallacin Abuja, Abdulkadir Salman Sholagberu ya bukaci yan Najeriya su koma ga Ubangiji kan tsadar rayuwa da ake ciki.
CBN ya yi karin haske kan kudin da za a rika cirewa idan mutum ya cire kudi ta ATM a bankin da ba shi da asusu. Za a rika cire N100 idan mutum ya cire kasa da N20000
Babban bankin Najeriya, CBN ya kawo sabon tsarin cajin kudi ta ATM. Za rika cire N100 kan kowane N20,000 idan mutum ya cire kudi ta ATM din da ba na bankinsa ba.
Dangote Peugeot ya fara hada Peugeot 3008 GT a Kaduna, yana shirin kaddamar da Landtrek 4x2, don bunkasa kasuwar motocin gida da habaka tattalin arzikin kasa.
Labaran tattalin arzikin Najeriya
Samu kari