Labaran tattalin arzikin Najeriya
Aliyu Sani Madakin-Gini daga jihar Kano a majalisar wakilan tarayya a babban birnin Abuja ya tasa sabon gwamnan CBN a gaba game da karfafa Legas da karyewar Naira
Kudirin lantarki ya zama doka bayan sa hannun Bola Ahmed Tinubu a yammacin Juma’a. Dokar ta haramta raba wutar lantarki tsakanin jihohi da kasa a Najeriya.
Jama’atu Nasrul Islam ta nuna damuwa kan matsalar hauhawan farashin kayayyakin abinci da ake fuskanta a Najeriya, tayi kira ga shugaba Bola Tinubu da masu mulki.
Kwamitin majalisar dattawa ya sanya gwamnan babban bankin Najeriya, Yemi Cardoso a gaba domin ya yi bayani kan halin da tattalin arzikin ƙasar na ke ciki.
Gwamnoni sun dauki matakai domin rage tsadar abinci a Najeriya. Mai girma gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya sa hannu a kan matsayar da abokansa suka dauka.
Daya daga cikin attajiran Najeriya, Abdul Samad Rabiu, ya yi asarar dala biliyan 2.7, sakamakon garambawul da gwamnatin Najeriya ta yi a fannin kudin kasar.
Sanata Ben Bruce ya ce a koma amfani da Glo domin kiran waya da hawa yanar gizo. Idan ba mu yi wadannan abubuwa uku ba, sai mu zo wata rana za a ji $1 za ta N5000.
Shugaba Bola Tinubu ya dawo gida lokacin da ake fama da tsadar rayuwa, lamarin da ya jawo zanga-zanga a wurare. Tinubu ya bada umarni tun daga Faransa kafin ya dawo.
Shugaba Bola Tinubu ya ce ya gaji tattalin arziki mai rauni, wanda dole yana bukatar garambawul domin an shafe shekaru da yawa da matsalar kudi da tulin bashi.
Labaran tattalin arzikin Najeriya
Samu kari