Labaran tattalin arzikin Najeriya
Za a samu labari jama'ar gari a Jihar Katsina sun daka wa wata motar kamfanin Dangote wawa, inda suka yi awon gaba da kayan abincin da take dauke da su.
Tsumagiyar kan hanya ta fyade har wadanda ke aiki a sakatariyar APC. Wahalar rayuwa ta jawo ‘yan jam’iyyar APC za suyi Abdullahi Ganduje da shugabanni zanga-zanga.
Tun da Bola Tinubu ya karbi rikon Gwamnatin Najeriya karin wahala da kuncin rayuwa ake ta shiga. Sanata Sani Musa ya nuna cewa tsare-tsaren APC ba su aiki.
Mansur Ibrahim Sokoto yana ganin babu dalilin gwamnati ta rika fada da ‘yan kasuwan da suka adana kayan abinci a Najeriya ya ce ba su ne su kawo tsadar rayuwa ba.
Farfesa Kabiru Isa Dandado ya ce janye tallafin man fetur ranar farko ya jawo tsadar rayuwa, ya ce idan yunwa tayi kamari, za a iya dibar jama’a a shigar da su barna
An bayyana jihohin Najeriya 10 da ake yawan fama da tsadar kayayyakin abinci a Najeriya. An bayyana dalilin da yasa kayayyakin ke kara tashi a halin yanzu.
Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Mista Olayemi Cardoso ya bayyana cewa duk duniya aiki guda daya tak ta fi tasa wahala a halin yanzu, ya bayyana hakan ne a Abuja.
Dillalan hatsi a kasuwar hatsi ta kasa da kasa ta Dawanau a jihar Kano sun karya farashin hatsi domin rage radadin da jama'a ke fuskanta a jihar.
Mun tattaro matakan da aka cin ma yayin da Bola Ahmed Tinubu ya zauna da Gwamnonin jihohi. Shugaban kasa ya yabi kokarin da Abba Kabir Yusuf ya fara a Kano.
Labaran tattalin arzikin Najeriya
Samu kari