Labaran tattalin arzikin Najeriya
Alhaji Aliko Dangote ya ce zuwa gobe Talata, 16 ga Disamba sabon farashin man fetur zai fara aiki bayan sauki da ya yi. Ya ce zai cigaba da saukakawa jama'a.
Gwamnatin tarayya ta bude shirin YouthCred wanda aka samar domin bai wa matasa masu aikin yi bashin kudi, an kaddamar da shirin ga kowane matashi.
Gwamnatin Najeriya ta hada kai da Faransa domin inganta tattara haraji. Sababbin dokokin harajin Najeriya na Bola Tinubu za su fara aiki a farkon 2026.
Cibiyar kididdiga ta kasa NBS ta fadi yadda farashin abinci ya yi kasa a watan Oktoban 2025. Abinci ya sauko a jihohi da dama, Yobe ta fi sauran jihohi arahar abinci
Gwamnatin Ahmad Aliyu ta amince da kashe Naira biliyan 8.4 domin sake gina babbar kasuwar Sokoto da gobara ta lalata, tare da amincewa da kasafin kudin 2026.
Gwamnatin Tarayya za ta karɓi bashin N17.89tn a 2026 saboda karuwar gibin kasafi da raguwar kudaden shiga, inda mafi yawan bashin zai fito daga cikin gida.
ECOWAS ta nada Dangote a matsayin shugaban farko na majalisar kasuwancinta domin karfafa zuba jari na cikin gida, bunkasa cinikayya da hada-hada a Yammacin Afrika.
Shugaban Majalisar Shari'a ta Najeriya, Dr. Bashir Aliyu ya ce mutane na kara natsuwa da harkokin bankin musulunci ne saboda yadda yake da adalci da kaucewa haram.
Gwamnatin Najeriya karkashin Bola Ahmed Tinubu ta karbi akalla dala biliyan 9.65 a matsayin bashi daga Bankin Duniya a tsakanin shekarar 2023 zuwa 2025.
Labaran tattalin arzikin Najeriya
Samu kari