Labaran tattalin arzikin Najeriya
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya gabatar da kasafin kudin jihar Legas na 2026. Ya mika kasafin Naira tiriliyan 4.2 a shekarar 2026 mai zuwa.
Kungiyar tarayyar Turai (EU) ta halarci wani taro domin karfafa mata a jihar Kano. EU ta goyi bayan shirin farfado da kamfanonin yadi a Kano wajen karfafa mata.
Jihar Kano ta shiga layin jihohin da suka taba gabatar da kasafin kudi na sama da Naira tiriliyan guda, jihar Legas ce ke ke jan ragama inda ta haura N3trn.
A labarin nan, za a ji cewa gwamnatin Kano ta sami nasarar inganta kudin shiga da ta ke samu a hukumar KANGIS daga Naira miliyan 50 zuwa Naira miliyan 750 a wata.
Gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi sun raba N2.094trn a watan Oktoba 2025, ƙasa da wannan aka samu a Satumba. Kudin shiga ya karu, VAT ya ragu sosai.
A wata na bakwai a jere, hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ta sauka zuwa 16.05% a watan Oktoba, 2025 idan aka kwatanta da watan Satumban da ya gabata.
A labarin nan, za a ji yadda kungiyar SERAP ta bukaci gwamnan babban bankin Najeriya, Olayemi Cardoso a kan ya yi bayani a kan bacewar N3trn daga bankin.
Farashin kayan abinci ya fadi warwas a Benue, lamarin da ya faranta ran masu saye amma ya jefa ’yan kasuwa da manoma cikin asara. Masana sun gargadi gwamnati.
Hukumar NPA ta tabbatar da cewa jiragen ruwa 20 sun iso Najeriya kuma sun fara sauke man fetur da kayan abinci a tashoshin Apapa, Tincan da Lekki da ke birnin Legas.
Labaran tattalin arzikin Najeriya
Samu kari