Hukumar yan sandan NAjeriya
'Yan sanda sun kama Nze Chinasa Nwaneri, tsohon mai baiwa Gwamna Hope Uzodimma na jihar Imo shawara kan ayyuka na musamman a wani otel da ke Owerrri.
Rundunar 'yan sanda a jihar Akwa Ibom ta tabbatar da sace basarake, Ogwong A Abang a jihar a daren jiya Asabar 18 ga watan Mayu bayan sun kutsa kai cikin fadarsa.
Rundunar yan sanda a jihar a Lagos ta tabbatar da mutuwar wani dattijo mai shekaru 50 a jihar da aka samu gawarsa bayan yaje kallon kwallo a birnin Ikeja.
Wasu matasa a jihar Enugu sun yi amfani da bindigar wasan yara wajen kwace motar wani mutum, amma sun shiga hannu bayan da 'yan sanda suka tasa su gaba.
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta bayyana cewa an samu ƙarin adadin waɗanda Allah ya yi wa rasuwa sakamakon harin masallaci a yankin Gezawa ranar Laraba.
Gwamnatin jihar Filato ta ba masu sayar da shanu wa'adin mako biyu domin su tashi daga kasuwar Kara da ke Bukuru. Yan kasuwar sun koka kan matakin.
Rundunar 'yan sanda a jihar Kwara ta cafke likita da kuma masu taimaka masa guda hudu kan zargin batar da mahaifa da kuma cibiyar jariri a jihar bayan haihuwarsa.
Yan sandar Najeriya sun kama gungun masu garkuwa da mutane a jihar Delta. Cikin mutane ukun da aka kama daya ya ce ya zo Najeriya ne daga kasar waje.
Rundunar ‘yan sanda a jihar Anambra ta ce ta kaddamar da farautar wadanda suka yi garkuwa da Basil Chukwuemeka, wani babban limamin cocin Katolika a jihar.
Hukumar yan sandan NAjeriya
Samu kari