Nasir Ahmad El-Rufai
Shugabannin APC da NNPP a mazabar Kargi a karamar hukumar Kubau sun koma jam'iyyar SDP. Ana ganin hakan na cikin tasirin Nasir El-Rufa'i a jihar Kaduna.
Yayin da 2027 ke karatowa, ‘yan siyasa na kokarin janyo Buhari cikin tafiyarsu, inda suke kai masa ziyara don neman goyon baya da tasirinsa a siyasar Arewa.
Atiku Abubakar da Nasir El-Rufa'i sun shiga yankin Naja Delta domin yada maganar hadakar 'yan adawa a 2027. 'Yan Neja Delta sun fara goyon bayan sabuwar tafiyar.
Wasu na hasashen shugaban kasa, Bola Tinubu na kokarin hana manyan ‘yan siyasa daga bangaren CPC ficewa daga jam’iyyar APC zuwa SDP kafin zaben 2027.
Wata kungiya mai suna Northern Conscience Movement (NCM) ta nuna shakku kan yadda Nasir Ahmed El-Rufai ya koma yana yin tsrayya da Atiku Abubakar a siyasance.
Sanata Muhammad Ali Ndume ya bayyana cewa ba shi da shirin sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa SDP, ya ce masu shirin hakan ba su sami abin da suke so bane.
Dan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya jagoranci tawagar manyan ‘yan adawa irin su Nasir El-Rufai wajen kai wa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ziyara.
Shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya ce za su nunawa 'yan adawa cewa sun shirya a zaben 2027. Ya yi raddi wa Atiku da El-Rufa'i kan hadakar 'yan adawa.
Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ce ziyarar da Atiku da tsofaffin gwamnoni suka kai wa Buhari a Kaduna ba ta da alaƙa da siyasa ko batun 2027.
Nasir Ahmad El-Rufai
Samu kari