Hadi Sirika
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin tsohon ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika, ɗiyarsa, da wasu mutane biyu kan N100m kowanne.
Yayin da EFCC ke shirye-shiryen gurfanar da shi, tsohon ministam sufurin jiragene sama, Hadi Sirika tare da ɗiyarsa sun isa harabar babbar kotun tarayya, Abuja.
Hukumar EFCC ta tabbatar da cewa za ta gurfanar da tsohon Ministan Buhari, Hadi Sirika a gaban kotu a gobe Alhamis 9 ga watan Mayu kan zargin wawushe N2.7bn.
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC) ta shirya gurfanar da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika a gaban kotu a mako mai zuwa.
Ministan Harkokin Jiragen Sama, Festus Keyamo zai shiga matsala kan bincikar badakalar kudade wanda wasu tsoffin ministocin Buhari suke ganin hakan zai gaba su.
Hukumar EFCC ta kulle asusun bankin dan uwan Ministan Buhari, Hadi Sirika mai suna Abubakar Ahmed Sirika dauke da biliyan uku kan badakalar biliyan takwas.
Festus Keyamo ya fadi irin kudin da gwamnati ta kashe a dalilin barin hedikwatar FAAN a Abuja. Ganin an kashe Naira biliyan 1 wajen zirga-zirga ya sa aka koma Legas.
Festus Keyamo ya ce EFCC tana binciken kwangilar Nigerian Air ana gudanar da binciken laifi a yanzu. Ana binciken Hadi Sirika a kan kwangilar Nigeria Air.
Mai taimakawa shugaban kasa wajen harkar manufofi da tabbatar da tsare-tsare, Hadiza Bala Usman ta ce akwai Ministocin tarayyan da Shugaba Tinubu zai rabu da su.
Hadi Sirika
Samu kari