Manyan Labarai A Yau
Shugaban ƙungiyar gwamnonin yankin Arewa maso Yamma, Dr. Dikko Umar Radda, ya bayyana cewa babu batun yin sulhu tsakaninsu da ƴan bindiga a yankin.
Sanata Shehu Sani ya ce bai kamata yan Najeriya su yi martani ba illa ihun amin ga hasashen Fasto Enoch Adeboye na cewa naira za ta kara karfi kan dala.
Wani bam da ƴan ta'addan Boko Haram suka dasa ya tashi da wasu mutane a jihar Borno. Bam ɗin dai ya yi sanadiyyar halaka mutum 12 yayin da wasu suka jikkata.
Majalisar wakilai ta dauki mataki domin kawo karshen rikice-rikicen da suka addabi jihar Plateau. Majalisar ta kafa kwamitin da zai gano musabbabin rikicin.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar halaka wani kasurgumin shugaban ƴan bindiga a jihar Zamfara. Sojojin sun kuma ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.
Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya yi magana kan gayyatar da Abdullahi Umar Ganduje ya yi wa Gwamna Abba ta shiga jam'iyyar APC.
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya sanya dokar hana fita a wasu kauyuka biyu na jihar. Gwamnan ya sanya dokar ne biyo bayan barkewar rikici.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya caccaki daya daga cikin abokan hamayyarsa, Atiku Abubakar bayan ya bukaci da ya yi murabus idan ba zai iya ba.
Sanata Kawu Sumaila ya ki amincewa da bukatar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na maye gurbin Babban daraktan dake kula da bangaren gas, Mansur Kuliya da Oluwole.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari