Tinubu Ya Yi Martani Kan Murabus Din da Atiku Ya Ce Ya Yi, Ya Aike Masa da Sako Mai Zafi

Tinubu Ya Yi Martani Kan Murabus Din da Atiku Ya Ce Ya Yi, Ya Aike Masa da Sako Mai Zafi

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi martani mai zafi kan buƙatar da Atiku ya nemi ta ya yi murabus
  • Tinubu ya bayyana cewa Atiku har yanzu bai gama warkewa daga ciwon jin zafin rashin nasarar da ya yi a zaɓen 2023 ba
  • Shugaban ƙasar ya bayyana cewa yana sane da halin da ake ciki kan matsalar tsaro kuma yana bakin ƙoƙarinsa don magance matsalar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu a daren Talata, 30 ga watan Janairu, ya caccaki ɗaya daga cikin manyan abokan hamayyarsa, Atiku Abubakar, bayan ya buƙaci ya yi murabus idan ba zai iya ba.

Tinubu, wanda ya bayyana kiran na Atiku a matsayin mara kan gado, ya ce yana kula da halin da ƙasar nan ke ciki.

Kara karanta wannan

An bukaci Tinubu ya katse ziyarar da yake a Paris ya dawo gida, an bayyana dalili

Tinubu ya yi martani ga Atiku
Tinubu ya yi wa Atiku martani mai zafi Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin Bayo Onanuga, mai baiwa Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, wacce Legit Hausa ta samu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A halin yanzu dai Shugaba Tinubu yana birnin Paris na ƙasar Faransa.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Maganar da Alhaji Atiku Abubakar ya yi na zargin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da yin tafiyarsa ana cikin ƙalubalen tsaro da tattalin arziki, abu ne da za a kira mara kan gado.
"Hakan na zuwa kwanaki kaɗan bayan ya yi wa shugaban ƙasa ƙazafi a kan batun karɓar lamunin da kamfanin NNPC ya yi, bayanin nasa na baya-bayan nan ya gaza kai abin da ake tsammani daga wajen dattijon ƙasa.
"Muna so mu yi amanna cewa har yanzu Alhaji Atiku bai warke daga shan kayen da ya yi a zaɓe ba, kuma yanzu ya koma neman kafar da zai riƙa kai wa Shugaba Tinubu hari.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fusata kan kisan da aka yi wa sarakunan gargajiya, ya bayar da sabon umarni

"Shugaba Tinubu bai yi tafiyar ba, ba tare da sanar da ƴan Nijeriya inda yake ba, ya bayyana cewa zai yi ziyara ta ƙashin kansa a Faransa tare da bayyana ranar dawowarsa.

Tinubu yana sane da halin da Najeriya ke ciki

Sanarwar ta cigaba da cewa:

"Yayin da yake ƙasar Faransa, Shugaba Tinubu yana bin diddigin abubuwan da ke faruwa a cikin gida, kuma yana kan gaba a halin da ake ciki a ƙasar nan.
"Ya kasance yana tuntubar jami’ansa da jami’an tsaro kuma ya umurce su da su kawar da duk wani nau’in aikata laifuka a ƙasar nan.
"Musamman ya umarce su da su kamo waɗanda suka aikata laifin kisan wasu sarakuna biyu a jihar Ekiti da kuma sace wasu ɗalibai a jihar.
"Idan har da gaske Alhaji Atiku ya damu da matsalar tsaro kuma ba siyasa yake yi ba, ya kamata ya san cewa Shugaba Tinubu na kan gaba kuma yana bakin ƙoƙarinsa wajen dawo da zaman lafiya a ƙowane bangare na ƙasarmu.

Kara karanta wannan

"Idan ba za ka iya ba ka sauka": Atiku ya caccaki Tinubu kan abu 1 tak

"Hukumomin tsaron mu na aiki tuƙuru don ganin an shawo kan matsalar tsaro. Shugaba Tinubu yana ba su dukkan goyon bayan da suke buƙata domin samun nasara a yaƙin da ake da masu aikata laifuka da kuma tabbatar da tsaron kowane yanki na ƙasarmu."

Omokri Ya Buƙaci Tinubu Ya Dawo Gida

A wani labarin kuma, kun ji cewa Reno Omokri ya shawarci Shugaba Tinubu da ya baro birnin Paris ya dawo gida Najeriya.

Tsohon hadimin na Goodluck Jonathan ya bayyana cewa ya kamata shugaban ƙasar ya dawo gida domin fuskantar matsalar tsaron da ake fama da ita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel