Lafiya Uwar Jiki
Rahotanni sun tabbatar da cewa masu 'bleaching' sun yi yawa a Najeriya inda Ministan Lafiya ya nuna damuwa kan yadda ake kara amfani da kayan gyaran fata a Najeriya.
NAFDAC ta rufe kantin magani a Abuja kan sayar da kayan magani marasa rijista. Kayayyakin sun kai na N7m, kuma an cafke mutane biyu domin bincike.
Gwamnatin Kogi za ta kashe N7bn don gyara cibiyoyin lafiya 88, tare da goyon bayan Babban Bankin Duniya, don inganta kiwon lafiya a jihar cikin watanni huɗu.
Likitocin ARD-FCTA ta gargadi Wike kan yajin aiki mafi muni idan ba a biya bukatunsu ba cikin kwanaki 14, ciki har da albashi, kudin kayan aiki, da gyaran dokoki.
Gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta fito da shirin tallafawa 'yan Najeriya wajen saya musu magani domin rage radadin matsin rayuwa saboda matsin tallali
Ma’aikatan lafiya a asibitin kwararru na Gusau na neman albashin wata shida, alawus, da karin girma ko shiga yajin aiki. Suna zargin ba a gyara albashinsu ba.
Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya bayyana takaicin yadda aka rika yada labarin cewa ya riga mu gidan gaskiya, alhali ya na nan da ransa.
An kwantar da mutane da dama a asibitoci daban-daban biyo bayan wani aikin duba lafiyarsu kyauta a garin Abiriba da ke karamar hukumar Ohafia ta jihar Abia.
Likitoci karkashin kungiyar likitocin Najeriya (NMA) sun sanar da shiga yajin aikin sai baba ta gani a asibitin Murtala Muhammad da ke jihar Kano.
Lafiya Uwar Jiki
Samu kari