Labarin Sojojin Najeriya
Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya kawo mafita kan yadda za a dakile matsalar tsaron kasar inda ya ce hadin kai ne kadai zai kawo karshenta.
Gwannatin jihar Katsina ta yi alhinin kisan da 'yan bindiga suka yi wa wani kwamandan sojoji a jihar. Ta bayyana cewa kisan da aka yi masa babban rashi ne ga jihar.
Hedkwatar tsaron Najeriya ta ce sojoji ba za su yi ƙasa a guiwa ba har sai sun ga bayan duk wani nau'in ta'addanci a faɗin ƙasar nan domin zaman lafiya ya samu.
Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka wasu 'yan ta'adda guda bakwai a yayin wani artabu da suka yi a jihar Sokoto. Sun kwato makamai.
Sarkin Kwatarkwashi a jihar Zamfara, Abubakar Ahmed Umar ya bayyana cewa 'yan ƙasashen ketare da kuma ma'adinai a Arewacin Najeriya ne silar matsaar tsaro.
An rahoto cewa sojojin da ke atisayen 'Whirl stroke' a jihar Taraba sunsamu nasarar kashe 'yan bindiga biyu yayin dakile wani harin da suka kai wani kauyen jihar.
Wasu mahara sun yi kwantan ɓauna, sun halaka babban kwamandan rundunar dojoji a yankin ƙaramar hukumar Kanƙara a jihar Katsina ranar Alhamis da ta wuce.
Rundunar sojojin ƙasa ta Najeriya ta bayyana cewa dakarunta sun yi nasarar kashe ƴan ta'adda uku, sun kamo biyu sannan sun kwato makamai a Sokoto, Kaduna da Filato.
Mazauna kauyen Allawa da ke karamar hukumar Shiroro a jihar Neja sun shiga fargaba bayan sojoji sun tattare kayansu a kauyen sun fice da safiyar yau Alhamis.
Labarin Sojojin Najeriya
Samu kari