Zaben jihohi
Dokar kasa tayi tanadi bayan duk shekaru hudu ayi zaben Gwamnoni, mun kawo jihohin da ‘yan takaran gwamnonin adawa a jihohi 28 ba su shigar da kara a bana ba.
Kotunan sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnoni na cigaba da zartar da hukuncinsu kan ƙararrakin da ke gabansu. Gwamnoni takwas za su san makomarsu a Oktoba.
Kotun sauraran kararrakin zaben a Nasarawa ta rusa zaben Gwamna Abdullahi Sule inda ta tabbatar da David Ombugadu na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zabe.
Rahoton da muke samu daga jihar Ogun ya bayyana yadda aka tabbatar da dan takarar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a zaben bana wato 2023.
Akalla mambobin jam'iyyun PDP da Labour dubu hamsin ne su ka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a jihar Bayelsa yayin da ake shirin gudanar da zabe a jihar.
Isa Ashiru Kudan, dan takarar zaben gwamna a jihar Kaduna ya bayyana cewa zai daukaka kara don kwato wa 'yan jihar hakkinsu inda ya ce ba don kashi ya ke yi ba.
Kotun sauraran kararrakin zaben jihar Kaduna ta yanke hukunci kan shari'ar da ake tsakanin Gwamna Uba Sani na jam'iyyar APC da kuma Isa Ashiru na jam'iyyar PDP.
A yau ne kotun sauraran kararrakin zaben jihar Kaduna ta shirya yanke hukunci tsakanin Isa Ashiru na PDP da Gwamna Uba Sani na APC, kotun za ta yi amfani da 'Zoom'.
Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Ebonyi ta zartar da hukuncinta kan zaɓen gwamnan jihar. Kotun ta tabbatar da nasarar gwamna Nwifuru na jam'iyyar APC.
Zaben jihohi
Samu kari