Kiwon Lafiya
Gwamnan jihar Borno ya sanar da fara biyan daliban jinya Naira dubu 30 duk wata a fadin jihar. Gwamnan ya bada sanarwar ne jiya Laraba a Maiduguri.
An samu rahoton barkewar wata sabuwar cuta a karamar hukumar Kura ta jihar Kano. Cutar wacce ba a san musababbabinta ba ta salwantar da rayukan mutum 45.
Gwamnan jahar Gombe, Inuwa Yahaya, ya sanar da dawo da dokar sharar karshen wata-wata domin tsaftace muhallin jahar da kiyaye lafiyar al'ummar jahar.
Duk da kokarin da Nasir El-Rufai ya yi a bangarori da yawa a Kaduna, akwai inda ake bukatar gyara. Gwamna Uba Sani ya ce asibitocin jihar Kaduna sun yi kaca-kaca.
Ana fargabar rasuwar mutane 4 a karamar hukumar Isa, jihar Sakkwato. Har yanzu hukumar NCDC ta ce ba a kai ga gano asalin cutar ba. Yara ne suka fi kamuwa
Hukumar kula da asibitoci ta jihar Kano ta dauki matakin ladabtarwa kan wasu ma'aikatan lafiya da aka samu sun cin zalin marasa lafiya a a asibitocin jihar.
Dr. Jabir Maihula ya ce duk wanda ke da lalura ta rashin lafiya zai rama azumi ko da ya yi ciyarwa, sai idan mutum ya tsufan ko rashin lafiyar da ba warkewa.
Majalisar wakilai za ta binciki ma'aikatar lafiya kan yadda ta kashe $300m da aka ware don yaki da zazzabin sauro. An nemi ministan lafiya ya gurfana gaban majalisar
An samu bullar cutar zazzabin Lassa a kananan hukumomi bakwai na jihar Bauchi yayin da hukumar NCDC ta ce sabbin mutane 96 sun kamu da cutar a jihohi 12 na kasar.
Kiwon Lafiya
Samu kari