Sirrika biyar na cikin dankalin hausa ga lafiyar jiki

Sirrika biyar na cikin dankalin hausa ga lafiyar jiki

A kasashen duniya da dama ana matukar noman dankalin hausa saboda amfanin da yake dashi a jiki.

Kwararru da masana ilimin sinadaren da ke cikin abinci suna shawartar mutane su yawaita cin dankalin domin amfana da sinadaren da dankalin da dauke da shi.

Ga wasu daga cikin amfanin da dankalin ke yi a jikin mutum:

1. Kawar da cutar daji

Dankalin hausa na dauke da sinadarai masu yaki da kwayoyin cuta 'antioxidant' wanda ke kare jiki daga kamuwa daga cutar daji.

2. Yana kara karfin kashi

Dankali na dauke da sinadarin Magnesium da ke taimakawa jikin dan adam wurin hutu inda an gaji kuma yana inganta buguwar zuciya da inganta jijiyoyi da kasusuwan jiki.

Yana kuma dauke da Potassium da ke kawar da cutar koda da kawar da kumburin ciki da taimakawa jiki amfani da sinadaren da ke cikin abinci

DUBA WANNAN: Jerin kasashe biyar da rabin masu fama da matsanancin talauci a duniya ke rayuwa - Rahoto

3. Yana kara karfin ido

Dankalin hausa na dauke da sinadarin Beta-carotene da jikin dan adam ke sauya ta zuwa Vitamin A da ke inganta lafiyar idanu da karfafa garkuwar jikin dan adam. Karancin Vitamin A a jiki mutum na haifar da wata cutar makanta da ake kira Xerophthalmia.

4. Kara lafiyar kwakwalwa

Cin dankalin hausa musamman mai jan launi yana inganta yadda kwakwalwa ke aiki.

Binciken da masana suka gudanar da dabobi ya nuna cewa sinadarin 'anthocyanins' da jan dankali ke dauke da shi yana inganta lafiyar kwakwalwa da kare shi daga cututuka duk da cewa ba a gudanar da nazirin kan 'yan adam ba.

5. Karfafa garkuwan jiki

Dankalin hausa mai jan launi yana daya daga cikin abinci masu dauke da sinadarin beta-carotene da ke taimakawa jikin mutum sarrafa Vitamin A.

Vitamin A na da matukar muhimmanci wurin inganta garkuwar jiki kuma bincike ya nuna karancin Vitamin A na da alaka da raguwar karfin garkuwar jiki.

Kazalika, yana taka muhimmiyar rawa wurin inganta lafiyar hanji da cikin dan adam inda abinci ke wucewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164