Labaran garkuwa da mutane
Masu garkuwa da ɗaliban jami'a da hadiman shugaban ƙaramar hukumar Kabba/Buhu a jihar Kogi sun nemi N10m a matsayin kun fansa, sun sauko daga N100m.
Wasu miyagun ƴan bindiga sun shiga har cikin gida, sun yi awon gaba da wani malami, Sheih Isma'il Gausi a Zaria da ke jihar Kaduna da daren ranar Laraba.
Rahotanni daga yankin karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna sun nuna cewa ɓarayin daji sun hallaka Magajin Garin Gefe da ke yankin Kufana da tsakar dare.
Yan bindiga sun yi ajalin mutane shida, sannan sun yi awon gaba da wasu mutane 26 a hare-haren da suka kai kauyuka huɗu a karamar hukumar Kauru ta Kaduna.
Hukumar da ke kula da harkokin matasa masu yiwa ƙasa hidima a Najeriya NYSC ta ayyana ɓatan kodinetan da ke kula da jihar Akwa Ibom tare da direbansa.
Yayin da rashin tsaro ya ke kamari, an gano yadda gwamnatin tarayya ta fitar da kudi masu nauyi domin yakar ta'addanci a sassan da ta'addanci ya yi katutu.
Rahotanni sun nuna cewa wasu ƴan bindiga da ba a san ko su waye ba sun yi awon gaba da shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Kabba/Bunu a jihar Kogi, Barista Dare.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun yiwa jami'an rundunar tsaron jihar Sokoto kwanton bauna. 'Yan bindigan sun hallaka mutum biyar tare da wasu manoma.
Gwamnonin Arewa ta yamma sun shirya taron zaman lafiya a Kaduna domin ba kwamishinonin tsaro horo kan yaki da yan bindiga. Gwamnan Kaduna ya kaddamar da taron.
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari