Labaran garkuwa da mutane
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga sanye da kayan Fulani sun kai hari Sagwari da ke Abuja, sun sace mutum 10. Sun kai harin karfe 7:30 na yammacin ranar Lahadi,
Wasu miyagun yan bindiga sun halaka magajin garin Wuro Musa da suka sace a jihar Taraba ranar Jumu'a. An kashe manomi tare da sace wasu kauyukan Kaduna.
Masu garkuwa da mutanen da suka sace Alhaji Mansoor Al-Kadriyar da yaransa shida sun tuntubi yan uwansu, inda suka bukaci a biya kudin fansa naira miliyan 60.
Tsagerun yan bindiga sun yi awon gaba da mai martaba Eze Samuel Agunwa Ohiri, a gaban gidansa da ke Orodo, karamar hukumar Mbaitoli ta jihar Imo.
Sanata Karimi na Kogi ta Yamma ya bayyana cewa sha'anin tsaro na neman faskara a mazaɓarsa cikin yan kwanakin nan musamman batun garkuwa da mutane.
Rahotanni daga yankin karamar hukumar Bwari a birnin tarayya ya nuna cewa yan bindiga sun yi garkuwa da yan uwan juna su bakwai, sun ji wa yan sanda biyu rauni.
Wasu miyagun yan bindida sun kai farmaki kauyuka uku a babban birnin Tarayya Abuja da jihar Neja, sun kashe mutane hudu tare da sace wasu akalla 39.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta cafke wani matashi mai suna Salisu Adamu bisa laifin sace wani dan uwansa Auwalu Aminu mai shekaru uku da haihuwa.
‘Yan bindiga za su hallaka daliban jami’ar Gusau da aka yi garkuwa da su. Nan da mako guda za a kashe daliban idan ba a fito da mutanensu da ke tsare ba.
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari