Malamin addinin Musulunci
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya nuna damuwa kan abin da ya faru a masallacin Larabar Abasawa a jihar Kano, ya umarci hukumomin tsaro su yi bincike.
Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya aike da sakon ta'aziyya yayin da aka rasa daya daga cikin dattawan jihar Gombe, Gidado Bello Akko a jiya Lahadi a Zariya.
Sheikh Sani Rijiyar Lemo ya gargadi Ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohanenye da ta cire hannunta game da aurar da mata marayu 100 a jihar Niger.
Hukumar Hisbah a jihar Kano ta hana maza masu aikin DJ gudanar da ayyuka a bukukuwan mata. Kwamandan Hisbah na jihar Kano sheikh Aminu Daurawa ne ya sanar.
Limaman Musulunci sun sha alwashin ci gaba da shirinsu kan aurar da mata marayu guda 100 da suka yi niyya a karamar hukumar Mariga a jihar Niger.
Abduljabbar Nasiru Kabara ya kori lauyan da ke karesa a kotun daukaka kara. Hakan yasa alkalin kotun daga shari'ar zuwa lokacin da zai samu wani lauyan.
Alhafiz Ismail Maiduguri ya ce masu mulki sun saye malamai, yake cewa ‘Malamai da fastoci sun ja kaya. Bayanan sun zo ne a wajen karatun littafi a Abuja.
Sheikh Adamu Muhammad Dokoro ya ce malaman da suka tallata APC su ankarar da shugabanni. A jawabin da ya yi a majalisin karatun, ya yi kira ga Bola Tinubu.
Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da lauyansa sun ki bayyana a zaman kotun da ya shigar yana kalubalantar hukuncin kisan da wata kotu ta yanke masa a Kano.
Malamin addinin Musulunci
Samu kari