INEC
Rahotanni sun bayyana cewa jam'iyyar APC ita ce a kan gaba bayan da hukumar zabe ta INEC ta bayyana sakamakon kananan hukumomi 13 na jihar Edo a ranar Lahadi.
Rahotanni sun bayyana cewa Gwamna Godwin Obaseki ya gaza ba jam'iyyar PDP nasara a karamar hukumarsa ta Oredo a zaben gwamnan jihar Edo da aka gudanar.
Ba a gama tattara sakamakon zaben jihar Edo ba, magoya bayan PDP sun durfafi ofishin INEC da ake tattara sakamakon zaben domin gudanar da zanga-zanga.
Rahotanni sun bayyana cewa Dan takarar gwamnan jihar Edo a karkashin jam’iyyar PDP Asue Ighodalo ya yi nasara a karamar hukumarsa ta Esan ta Kudu maso Gabas.
Nan da 'yan awanni za a san wanene zai zama sabon gwamna a jihar Edo inda ake zabe. INEC ta yi maganar soma tattara sakamako, a san wanda ya lashe zaben Edo.
Rahotanni daga cibiyar tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Edo da ke da zama a birnin Benin ta sanar da cewa PDP ta samu kuri'u 5,311 a Ovia ta Arewa maso Gabas.
Rahotanni daga cibiyar tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Edo da ke Benin City na nuni da cewa jam'iyyar APC ta lashe zabe a karamar hukumar Esan ta Yamma.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta fara tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Edo da aka gudanar a ranar Asabar, 21 ga watan Satumban 2024.
Rahotanni sun bayyana cewa jam'iyyar PDP ta fara samun nasara a zaben gwamnan jihar Edo yayin da hukumar INEC ta fara tattara sakamakon zaben na jiya.
INEC
Samu kari