Kai Tsaye: Yadda shirye-shiryen zaben gwamnan jihar Ekiti ke gudana

Kai Tsaye: Yadda shirye-shiryen zaben gwamnan jihar Ekiti ke gudana

A ranar Asabar, 18 ga watan Yuni, 2022 hukumar zabe ta kasa watau INEC za ta gudanar da zaben gwamnan jihar Ekiti.

Wa'adin gwamnan jihar, John Kayode Fayemi, na jam'iyyar APC ya zo karshe kuma al'ummar jihar zasu zabi wanda zai gajesa.

Yan takaran mafi shahara sune:

1. Bisa Kolawa na jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP

2. Biodun Oyebanji na jam'iyyar All Progressives Congress APC

Legit Hausa za ta kawo muku bayanai kai tsaye daga yadda shirye-shirye ke gudana, yadda zaben ke gudana har zuwa bayan sanar da wanda ya lashe.

Yarjejeniyar zaman lafiya

Shugaban hukumar INEC na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu ya sa hannu a matsayin shaida a wajen sa hannu a yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin ‘yan takarar gwamnan jihar Ekiti.

Wannan taro ya gudana a garin Ado Ekiti, jihar Ekiti da nufin ganin magoya bayan ‘yan takaran ba su tada zaune tsaye a zaben sabon gwamnan da za a gudanar a karshen makon nan ba.

Dan takara ya janye daf da zabe?

Rade-radi su na yawo a shafukan sada zumunta cewa Injiniya Segun Oni ya janye takararsa na neman zama gwamnan jihar Ekiti a karkashin jam’iyyar SDP.

Amma rahoton da ya fito daga The Cable, ya nuna har yanzu Oni yana takara. Kakakin SDP a Ekiti, Gani Salau, ya yi watsi da wasikar da aka fitar a ranar Juma’a.

“Ta ya mutum zai fita daga takara a ranar zabe? Aikin ‘yan adawa ne.” - Gani Salau.

Masu takara sun yi nasara a akwatinsu

Rahoton Premium Times ya bayyana cewa Abiodun Oyebanji mai takarar gwamnan Ekiti a jam’iyyar APC ya yi galaba a akwatinsa da ke Igede Ekiti.

Abiodun Oyebanji ya samu kuri’a 81 a rumfar da ya kada zabe. ‘Dan takarar PDP, Bisi Kolawole ya samu 23, sai Segun Oni na jam’iyyar SDP ya na da 30.

A Ifaki Ekiti inda Segun Oni ya jefa kuri’arsa, SDP ta samu kuri’u 218. Daily Trust ta ce jam’iyyar APC ta samu kuri’a 15, shi kuma Kolawole ya kare da biyu.

Muhimman bayanai kan jami'an INEC da zasu jagoranci zaben gobe

Muhimman bayanai kan jami'an INEC da zasu jagoranci zaben gobe

Adadin shugabannin akwatin zabe da mataimakansu PO's da APO's - 10,269

Adadin masu lura da shugabannin akwatin zabe SPO's - 245

RAC's na gundumomi - 177

Baturan zaben kananan hukumomi - 16

Baturen zaben jihar gaba daya - 1

Jami'an tsaro sun yi carko-carko a hedkwatar 'yan sandan Ekiti gabanin zaben gwamnan jiha

Wasu hotuna da jaridar Vanguard ta yada sun nuna lokacin da jami'an tsaro ke tsaye carko-carko a bakin hedkwatar 'yan sanda ta jihar Ekiti gabanin zaben gobe Asabar na gwamnan jihar.

Rahoton da muka kawo a baya ya bayyana cewa, an tura dandazon jami'an tsaro zuwa jihar domin kula da sanya ido kan zaben da zai gudana a ranar 18 ga watan Yuni.

Jami'an tsaro sun taru a bakin hedkwatar 'yan sandan Ekiti
Kai Tsaye: Yadda shirye-shiryen zaben gwamnan jihar Ekiti ke gudana | Hoto: Vanguard News
Asali: Facebook

INEC ta tura muhimman kayayyakin zabe zuwa kananan hukumomi 16 na Ekiti

A ci gaba da ake na shirye-shiryen zaben gwamnan jihar Ekiti, hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta kai duk wasu muhimman abubuwa na zabe zuwa kananan hukumomi 16 na jihar.

Wani bidiyon da muka samo daga gidan talabijin na TVC ya nuna lokacin da jami'ai ke aikin kula da kuma jigilar kayayyakin.

Kafin nan, wani bidiyon ya sake nuna lokacin da jami'an INEC na jihar ke sanya hannu kan takardun da suka cancanci tafiya kafin a tafi dasu zuwa cibiyoyin zabe na kananan hukumomin.

Ekiti 2022: Yan takarar kujerar gwamna 11 sun kulla yarjejeniyar zaman lafiya

Masu neman takarar kujerar gwamna karkashin jam'iyyun siyasa guda 11 sun kulla yarjejeniyar zaman lafiya a tsakaninsu.

Sai dai kuma akwai wasu jam'iyyu biyar da yan takararsu basu halarci taron ba wanda ya gudana a garin Ado Ekiti, babbar birnin jihar Ekiti, jaridar The Cable ta rahoto.

Yan takarar da suka shiga yarjejeniyar sun hada da na jam'iyyun:

1. APC

2. SDP

3. ADC

4. NNPP

5. APP

6. ADP

7. AAC

8. NRM

9. PRP

10. ZLP

11. APGA

Jam’iyyun da basu halarci taron ba sune:

1. PDP

2. YPP

3. LP

4. AP

5. APM

Online view pixel