INEC: Yan Najeriya Na Son Ma'aikatan Mu Su Bi Su Har Gida Su Kai Musu Katin Zabe

INEC: Yan Najeriya Na Son Ma'aikatan Mu Su Bi Su Har Gida Su Kai Musu Katin Zabe

  • Hukumar zabe mai zaman kanta INEC reshen Jihar Legas ta koka kan yadda masu zabe suke kin zuwa karbar katin zabe
  • Kwamishinan hukumar na Legas, Olusegun Agbaje, ya ce cikin mutum 34,000 da suka yi rajista daga Yuni zuwa Disambar bara, 3000 kadai suka karbi katin
  • Agbaje ya ce ya umurci ma'aikatansu a kananan hukumomi su kira mutane don su taho su karba amma wasu cewa suka yi a biyo su gida a kawo musu katin, ya ce hakan ba zai yi wu ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Legas - Cikin sabbin masu zabe 34,000 da suka yi rajista daga watan Yuni zuwa Disamba a Legas, 3,000 kawai suka karbi katin zabensu na dindindin (PVC) a cewar kwamishinan zabe na Legas, Olusegun Agbaje.

Agbaje ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai wurin wani taron wakoki da aka yi don wayar da kan matasa kan zabe a Tafawa Balewa Square Legas, yana mai nuna rashin dadinsa kan rashin karban katin, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

2023: Mace Guda Da Ke Takarar Shugaban Kasa a APC Ta Janye Wa Tinubu, Ta Bayyana Dalili

INEC: Yan Najeriya Na Son Ma'aikatan Mu Su Bi Su Har Gida Su Kai Musu Katin Zabe
Yan Najeriya Na Son Ma'aikatan Mu Su Bi Su Har Gida Su Kai Musu Katin Zabe, INEC. Hoto: @daily_trust.
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu masu zaben cewa suka yi jami'an mu su kai musu katinsu gida, INEC

Ya kara da cewa hukumar ta umurci jami'anta a kananan hukumomi su kira masu zabe su fada musu su taho su karbi katinsu amma ba su samun amsa gamsassu, wasu masu zaben ma cewa suke yi a kawo musu PVC din gidansu.

The Punch ta rahoto cewa ya bada shawarar cewa ya kamata mutane su yi sadaukarwa don karban katin zabensu.

Ya ce:

"Muna da sabbin PVC guda 34,000, wadanda suka yi rajista daga Yuni zuwa Disambar bara, da suka yi rajista karon farko, katinsu ya fito amma abin damuwa tun Afrilun bara muka kawo katin amma zuwa ranar Litinin na makon da ta gabata, 3000 kadai suka karba katin.
"Na umurci ma'aikatan mu a kananan hukumomi su kira su don fada musu an kawo PVC dinsu, sun ce a kai musu gidajensu kuma hakan ba zai yi wu ba, ya zama dole ka sadaukar da lokaci. Na sha fada, ba za ka iya cin soyayyen kwai ba sai ka fasa kwan, idan hakan gaskiya ne sai mutane sun yi himma kafin karban katinsu na PVC".

Kara karanta wannan

Gwamna Bagudu ya bayyana dan takarar da za a kaddamar a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin APC

Ya jadada cewa hukumar za ta fara gangamin wayar da kan mutane su tafi su karbi katinsu daga watan Yuli.

A wurin taron, wakiliyar EU, Mrs Laolu Olaoye ta yaba wa hukumar ta INEC kan goyon bayan taron tana mai cewa an yi hakan ne don karfafa wa matasa gwiwa su rika shiga harkar zabe a dama da su.

2023: Mace Guda Da Ke Takarar Shugaban Kasa a APC Ta Janye Wa Tinubu, Ta Bayyana Dalili

A wani rahoton, yar takarar shugaban kasa, Uju Ohanenye, ta janye wa jagoran jam'iyyar All Progressives Congress, APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Ta sanar da hakan ne wurin taron jam'iyyar a ranar Talata a birnin tarayya Abuja, The Punch ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel