Da Dumi-Dumi: Majalisar Wakilai ta ƙasa ta yi garambawul a sabon kundin zaɓe 2022

Da Dumi-Dumi: Majalisar Wakilai ta ƙasa ta yi garambawul a sabon kundin zaɓe 2022

Abuja - Majalisar wakilan tarayya ta amince da garambawul a kundin zaɓe 2022 domin bai wa zaɓaɓɓun shugabanni da ke kan madafun iko damar sauke nauyin su a wurin tarukan jam'iyyu da zaɓen fidda gwani.

The Nation ta rahoto cewa Majalisa ta amince da wannan gyara ne a sashi na 84 bayan yin nazari kan kudiri mai taken, "Kudirin garambawul ga dokar kundin zaɓe No. 13 2022 da abin da ya shafi haka."

Kakakin majalisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila.
Da Dumi-Dumi: Majalisar Wakilai ta ƙasa ta yi garambawul a sabon kundin zaɓe 2022 Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Honorabul Abubakar Hassan Fulata shi ne ya ɗauki nauyin gabatar da kudirin gaban takwarorinsa na majalisa kuma suka amince da shi a yau Laraba.

Wannan mataki na zuwa ne awanni 24 bayan majalisar Dattawa ta ƙasa ta amince da yi wa kundin garambawul irin wannan.

Ƙarin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262