INEC ta baiwa Atiku, Tinubu, Kwankwaso mako 1 su mika mata sunayen mataimakansu

INEC ta baiwa Atiku, Tinubu, Kwankwaso mako 1 su mika mata sunayen mataimakansu

  • Hukumar shirya zabe ta bayyana ranar karshen mika mata sunayen yan takarar shugaban kasa da mataimakansu
  • INEC tace dukkan jam'iyyu su daura sunayen yan takararsu a shafinta na yanar gizo da ta shirya
  • Gwamnoni da yan majalisun dokoki an baiwa jam'iyyu wata guda cir don daura sunayensu

FCT Abuja - Hukumar gudanar da zabe ta kasa watau INEC ta bayyana ranar karshe ga jam'iyyun siyasa na mika mata takaran shugaban kasa da mataimakansu.

Hukumar tace nan da ranar Juma'a, 17 ga watan Yuni misalin karfe 6 na yamma, za'a rufe karbar sunan.

Amma na gwamnoni da yan majalisar dokokin tarayya, an basu nan da ranar 15 ga watan Yuli, 2022.

Hukumar INEC
INEC ta baiwa Atiku, Tinubu, Kwankwaso mako 1 su mika mata sunayen mataimakansu Hoto: @inecnigeria
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyar ADC Ta Zabi Dan Takarar Shuagban Kasa, Ya Yi Alkawarin Yi Wa Tinubu Da Atiku Ritaya

Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana hakan a ganawarsa da kwamishanonin INEC na jihar REC ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja.

Yace:

"Yau Alhamis, 9 ga watan Yuni, 2022 ne ranar karshen gudanar da zaben fidda gwanin dukkan jam'iyyun siyasa."
"Cikin mako daya fari daga gobe 10 ga Yuni, 2022, dukkan jam'iyyu zasu aika sunayen yan takaransu (Shugaban kasa/Mataimakisa, Sanatoci da majalisar wakilai) zuwa ranar Juma'a, 17 ga Yuni, 2022."

Farfesa Yakubu ya kara da cewa su kuma Gwamnoni da yan majalisar dokokin tarayya, nan da ranar 15 ga Yuli, 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel