Tsadar Mai
Gwamnatin jihar Kwara ta ba da umarnin samar da bas bas musamman a cikin birni domin zirga-zirgar jama'a zuwa wurare daban-daban bayan karin farashin man fetur.
Karin kudin man fetur da kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya yi, ya jawo masu sana'ar adaidaita sahu da sauransu sun yi karin kudi ga fasinjoji a Kaduna.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu gidajen mai na kamfanin NNPCL sun kara kudin litar mai daga N568 zuwa N855 har N897 a wasu wuraren da aka tabbatar.
Mutane da dama sun nuna farin cikinsu yayin da matatar man Aliko Dangote ta shirya samar da man fetur a fadin kasar domin saukakawa al'umma yayin da ake tsadar mai.
A wannan labarin za ku ji cewa mazauna jihar sun ce yanzu ba sa iya cin abinci sau uku a rana, wannan ya biyo bayan hauhawar farashin kayan abinci da ake samu.
A wannan labarin, za ku ji cewa kungiyar lauyoyi mata musulmi sun ce matsalar rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arziki ya fi shafar mata, an nemi daukin Tinubu.
Ewi na Ado-Ekiti, Oba Rufus Adejugbe ya haramta kungiyoyin 'yan kasuwa da ke tsauwalawa mutane kan tsadar kaya tare da kayyade farashin kayan abinci.
Wani matashin mai suna Maleek Anas ya wallafa a shafin X cewa ya sayi buhunan siminti guda biyu kan kudi N6,000 kowane daya daga kamfanin Dahiru Mangal.
Yayin da ake cikin wani irin mayuwacin hali a Najeriya, an gudanar da addu'o'i da karatuttukan Alkur'ani mai girma domin neman mafita a jihar Kano.
Tsadar Mai
Samu kari