Babban kotun tarayya
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba da umarnin cafke tsohon hafsan sojojin ruwa a Najeriya, Vice Admiral Usman Jibrin kan badakalar N1.5bn da wasu mutane biyu.
Wata kotu a Kano ta dakatar da kamfanin KEDCO da hukumar NERC tilastawa kamfanoni biyan sabon kudin wutar lantarki har sai kotu ta kammala sauraron karar.
Wata kotu a Amurka ta samu tsohon shugaban Binance Chanpeng Zhao da laifin bari a yi amfani da dandalinsa wajen almundahanar kudade. An daure shi wata 4
Babban bankin kasa, ya umarci bankunan yanar gizo daga yi wa sabbin kwatomomi rajista, yayin da ake zargin haramtacciyar hada-hada kamar halarta kudin haram
Wani tsohon ma'aikacin babban bankin Najeriya (CBN), ya bayyana a gaban kotu yadda ya karbowa Godwin Emefiele cin hancin $600,000 lokacin da yake jagorantar bankin.
Babbar kotun jihar Kano ta dage shari'ar tsohon gwamnan Kano, Abullahi Ganduje da ake zargin ya hada kai da iyalansa da wasu sun aikata zamba da karbar rashawa.
Babbar kotun tarayya ta yanke hukunci kan karar da 'yan shi'a suka shigar na zargin 'yan sanda sun kashe masu yara uku a Zariya. Kotu ta ci tarar wadanda ake kara.
Kungiyar SERAP ta shigar da kara kan kamfanin mai na Najeriya (NNPCL) kara a gaban kotu kan bacewar $2.04bn da N164bn na kudaden shigar man fetur.
Babbar kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta dakatar da wadanda ke kiran kansu shugabannin jam'iyyar APC kan sake daukar wani mataki kan Abdullahi Ganduje.
Babban kotun tarayya
Samu kari