
Gwamnatin Najeriya







Gwamnatin tarayya ta nada kwamishinonin haraji da za su warware rikici da tabbatar da ba wanda ya kaucewa biyan haraji a Najeriya. Wale Edun ne ya tabbatar da haka.

Kwamandan sojin Amurka a Afrika, Janar James Hecker ya ce za su dawo kai farmaki kan Boko Haram da saurann 'yan ta'adda a Afrika domin samar da tsaro.

Gwamnatin Tarayya ta raba dala miliyan 68.36 ga jihohi 28 a ƙarƙashin shirin SABER don inganta kasuwanci, sauƙaƙa dokoki, da jawo zuba jari a Najeriya.

Gwamnatin Donald Trump za ta binciki tallafawa Boko Haram da kidin USAID bayan Sanatan Amurka ya bankado bayanai. Amurka ta yi Allah wadai da Boko Haram.

Gwamnatin tarayya ta bukaci ‘yan kasuwa su rage farashin kayan abinci yayin da ta tallafa wa manoman Jigawa da kayayyakin noma na Naira biliyan 5.

'Yan Najeriya masu shiga kasar Nijar da fasfon ECOWAS sun fara fuskantar kalubale da aka fara dakatar da su. Ana zargin ana dawo da wasu zuwa gida Najeriya.

Dan majalisa, Hon. Philip Agbese ya karyata zargin da shugaban kamfanin Binance, Tigran Gambaryan ya yi masa ne neman a ba shi cin hanci da rashawa.

Kungiyar 'Arewa Consultative Forum' ta ce samar da hukumomin raya shiyyoyin Arewa maso Gabas da Yamma za su tallafa wajen ceto yankin daga durkushewa.

Dr Usman Bugaje ya ce mulkin shugaba Buhari da Bola Tinubu bai tsinana komai ga Najeriya ba. Ya ce APC ta zamo annoba ga Najeriya wajen gaza gyara kasa.
Gwamnatin Najeriya
Samu kari