Nade-naden gwamnati
Kwamishinan ilimi na jihar Rivers, Farfesa Prince Chinedu da kwamishiniyar gidaje, Gift Worlu (PhD) su ne sabbin kwamishinonin da suka yi murabus a ranar Juma'a.
Wutar rikici a jihar Rivers ta kara ruruwa yayin da kwamishinoni hudu suka yi murabus a ranar Alhamis. Kwamishinonin na goyon bayan Wike maimakon Gwamna Fubara.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya tsige akalla manyan jami’an gwamnati tara a cikin sa’o’i 24. Yawancinsu gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ce ta nada su.
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya sallami Kabir Mohammed da Tayyib Odunowo a matsayin shugabannin FAAN da NAMA tare da maye gurbinsu da wasu nan take.
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya sallami dukkan daraktocin ma'aikatar harkokin jiragen sama kwana daya bayan korar shugaban hukumomin FAAN da NAMA a jiya Laraba.
Gwamnatin jihar Kebbi ta sha alwashin korar duk wani kwamishina da ya siyar da motar da gwamnatin ta ba shi. Akalla kwamishinoni 26 ne suka samu kyautar mota.
Ma'aikatar bunkasa ma'adanan Najeriya ta roki majalisar tarayya da ta kara mata Naira biliyan 250 a kasafin kudin 2024 da za a ba ta. A yanzu an ba ma'aikatar N24bn.
Gwamnan jihar Katsina, Umaru Dikko Radda ya nada tsohon soja, Ahmad Daku a matsayin sabon shugaban hukumar Hisbah a jihar tare da nada kwamandansa.
Ministoci sun roki Majalisa ta kara masu kudin da za su kashe a 2024. Akalla Ministoci 3 su ka nuna kasafin kudin shekarar 2024 da aka yi ba zai je ki ina ba.
Nade-naden gwamnati
Samu kari