Nade-naden gwamnati
Bola Tinubu ya karawa kananan Ministoci girma, sababbin ministocin tarayya sun shiga ofis da kafar dama. Akwai kananun ministoci a majalisar da ta kunshi mutane 48.
Gwamnan Edo, Godwin Obaseki ya rusa majalisar zartarwa da sauran masu mukamai a gwamnatinsa yayin da yake kwanakin karshe na wa'adinsa na biyu a matsayin gwamna.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba zai sallami kwamishinoni da ba su tabuka komai ba domin kawo wasu sababbin jini.
Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya umarci a gaggauta gyara tashar wutar lantarki, yayin da kamfanin TCN ya gargadi cewa tashar wutar na iya sake lalacewa
Sabon ministan ma’aikatar dabbobi, Alhaji Idi Mukhtar Maiha, ya ce aikin da zai fara aiwatarwa shi ne tabbatar da zamanantar da harkar kiwo a kasar nan.
Gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji ya maye gurbin shugaban alkalan jihar wanda Allah ya yi wa rasuwa bayan doguwar jinya ranar 4 ga watan Nuwamba, 2024.
Ministan kudi da harkokin tattalin arziki, Wale Edun ya jaddada cewa tallafin mai ya tafi kenan har abada, ba gud] da ja da baya game da manufofin Bola Tinubu.
Shugaban ƙasa Bola Aed Tinubu ya faɗawa sababbin ministoci cewa su tabbaci haƙiƙa ƴan Najeriya za su rika zaginso to amma su jajirce kan aikin da aka ɗora masu.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa kwamishinan INEC mai kula da shiyyar Arewa maso Yamma, sanan ya nada wanda zai maye kuejrar REC na jihar Ogun.
Nade-naden gwamnati
Samu kari