Nade-naden gwamnati
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya nada sabon Akanta Janar na Tarayya. Shugaban Tinubu ya nada Shamseldeen Ogunjimi domin ya rike wannan mukamin.
Mudashiru Obasa ya koma matsayin kakakin majalisar Legas bayan murabus din Mojisola Meranda, lamarin da ake ganin zai iya kawo karshen rikicin siyasa a majalisar.
Bayan sanar da rasuwar tsohuwar minista a Najeriya, Shugaba Tinubu ya jajanta wa iyalan Adenike Ebunoluwa Oyagbola wacce ta rasu tana da shekara 94 a duniya.
Bayan sanar da rasuwar tsohuwar minista a Najeriya, Chif Adenike Ebun Oyagbola, Gwamna Dapo Abiodun ya nuna alhinin game da rasuwar mace ta farko da ta zama minista.
Hukumar alhazai ta kasa, NAHCON ta fitar da sanarwa kan daukar ma'aikatan lafiya domin aikin hajjin bana. Za a fara daukar ma'aikata a ranar 8 ga watan Maris.
Bayan kalaman Nasir El-Rufai kan hana shi mukamin Minista a gwamnatin Bola Tinubu, hadimin shugaban ya mayar da martani inda ya ke ba tsohon gwamnan shawara.
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya ba Sanata Sulaiman Hunkuyi mukami a Hukumar Ayyukan Majalisa (NASC) da ke wakiltar Arewa maso Yamma kwanaki biyar bayan komawa APC.
Ministan tattalin arziki da tsare-tsare, Alhaji Atiku Bagudu ya ce shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ba ya warware tsakanin shiyyoyin kasar nan wajen aikin ci gaba.
Majalisar dokokin Benue ta tsige Babban Alkalin Jihar, Maurice Ikpambese, bisa zargin take dokoki, cin hanci, da karkatar da kudaden shari’a bayan kuri’a.
Nade-naden gwamnati
Samu kari