Yan bindiga
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Zamfara. Miyaguk sun yi awon gaba da mutane zuwa cikin daji tare da kashe wasu daban.
Yan bindiga sun kuma kai hari a jihar Kogi inda suka kashe matasa uku da ake zargin ‘yan sa-kai ne a Ofoloke bayan sace basarake a garin kwanaki kadan baya.
Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Ikorodu a jihar Legas, Babajimi Benson, ya bayyana ba kananan hukumomi 'yancin cin gashin kai zai magance rashin tsaro.
Rahotanni sun tabbatar da cewa yan bindiga da suka sace shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Ose a Ondo, Nelson Adepoyigi sun hallaka shi da gangan.
Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da cewa ƴan bindiga sun farmaki shingen bincike a yankin mahaifar mai girma gwamnan jihar Anambara, Farfesa Charles Soludo.
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun sake kai harin ta'addanci a jihar Plateau. Miyagun sun hallaka mutane takwas a harin da suka kai a cikin dare.
Bayan harin yan bindiga a Bauchi, Gwamna Bala Mohammed ya tabbatar da mutuwar ‘yan bindiga fiye da 60 a harin da ya faru a kauyen Mansur na karamar hukumar Alkaleri.
'Yan sanda sun kama Fatima Salisu a Nasarawa da harsasai 481, ana zargin tana safarar su ga ’yan ta’adda a Katsina. Yanzu haka dai ana ci gaba da bincikarta.
Dan majalisar wakilai daga jihar Zamfara ya ce 'yan bindiga sun ba karnukansu jariran da aka haifa sun cinye su a cikin daji. Ya ce wata mata ne ta haife su a daji.
Yan bindiga
Samu kari