Yan bindiga
Rundunar ‘yan sandan Katsina da hadin gwiwar sojoji da KSCWC sun dakile hare-haren ‘yan bindiga a kauyukan Faskari, an fatattaki miyagun su ba tare da asara rai ba.
Masanin tsaro, Sani Shinkafi ya zargi gwamnatin tarayya da dakile yunkurin kama Bello Turji ko kashe shi a Zamfara duk da cewa CJTF sun kusa gamawa da shi.
An samu asarar rayuka bayan wani rikici ya barke tsakanin jagororin 'yan bindiga a Zamfara. Lamarin ya auku ne bayan an gwabza fada tsakanin bangarorin biyu.
Yayij da al'umma ke ƙara shiga damuwa kan matsalar tsaron da ake fama da ita a Arewa, Sani Black, wani kasurgumin ɗan bindiga ya nemi harajin zinare a Zamfara.
A labarin nan, za a ji cewa Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya ƙaryata cewa gwamnatinsa ta riƙa biyan ƴan ta'adda kuɗin fansa don ceto mutanen da aka sace.
Gwamnatin jihar Katsina ta shirya kashe kudade don inganta tsaro a manyan asibitoci. Gwamnatin za ta gina katangu a wasu manyan asibitoci saboda rashin tsaro.
A labarin nan, za a ji yadda gungun ƴan ta'adda su ka dawo aiki gadan-gadan, inda suke lashe mutane kamar kiyashi a sassan Katsina bayan jama'a sun fara samun sauƙi.
'Yan bindiga sun tafka ta'asa a jihar Sokoto bayan sun farmaki manoma. Miyagun sun hallaka manoman da ke tsaka da aiki a cikin gonakinsu a wani kauye.
Rundunar ‘yan sanda a Katsina ta dakile hare-hare biyu da aka kai a Sabuwa, inda ta ceto mutum 28. Amma 'yan ta'adda sun kashe mutane uku a harin.
Yan bindiga
Samu kari