Yan bindiga
Hakimin Ɗan Isa ya tabbatar da cewa ƴan bindiga sun fara karɓar haraji kafin su bari a yi noma a daminar bana a kauyuka 35 da ke yankinsa a jihar Zamfara.
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kan dakarun sojoji a jihar Katsina. 'Yan bindigan sun hallaka soja tare da raunata wasu jami'ai.
Dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da tsaro sun samu nasarar hallaka dakile wani harin 'yan bindiga a Katsina. Sojojin sun kuma ceto wasu mutanen da aka sace.
Sojojin Najeriya sun tarwatsa bikin 'yan bindiga da ruwan bama bamai yayin da suke tsaka da bikin aure a dajin Zamfara. An kashe 'yan ta'adda da dama a farmakin.
A labarin nan, za a ji cewa mazauna Zamfara sun shiga tashin hankali bayan wasu ƴan bindiga sun yi awon gaba da basarake jim kaɗan bayan korarsu daga yankin.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar dakile wani mummunan harin 'yan bindiga a jihar Zamfara. Sojojin sun kuma kwato makamai daga hannun tsagerun.
Gwamnatin jihar Zamfara ta tabbatar da cewa ƴan bindiga sun kai hare-hare kan jama'a a kauyuka daban-daban cikin kwanaki huɗu, ana fargabar sun sace 150.
Mai fashin baki kan lamuran tsaro, Alhaji Sani Shinkafi ya ce tattaunawar da aka yi da Bello Turji ba ta da amfani, inda ya bayyana ta a matsayin rashin adalci.
Yayin da ake maganar haɗaka da Bello Turji, Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah ya bayyana damuwa kan yadda ta'addanci ke kara ta'azzara musamman a yankin Arewa.
Yan bindiga
Samu kari