Yan bindiga
Wani hari da ake zargin ‘yan bindiga ne ya yi ajalin DPO, CSP Muhammad Sani Sagir, a karamar hukumar Rimi ta jihar Katsina ranar Juma’a 13 ga watan Fabrairun 2026.
Majalisar dokokin jihar Kaduna ta yi martani kan rahotannin da ke cewa 'yan ta'adda sun yi garkuwa da daya daga cikin mambobinta. Ta ce labarin kanzon kurege ne.
Sojojin Najeriya sun ceto wasu mutane takwas da aka sace a wajen biki a jihar Kano. 'Yan bindiga sun saka kayan sojoji sun sace mutanen a karamar hukumar Shanono.
'Yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a wani kauyen jihar Benue. Tsagerun sun hallaka jami'an tsaro na 'yan sanda tare da fararen hula yayin artabu.
Hukumar DSS ta gargadi 'yan sanda kan yiwuwar sabon hari a Gbabe, bayan kisan Woro. Gwamna AbdulRazaq ya kira taron gaggawa don inganta tsaro a Baruten.
Rundunar ‘yan sanda a jihar Adamawa ta cafke matasa uku da ake zargi da garkuwa da Alhaji Ahmadu, tare da gano ɗan mutumin da aka sace a cikin su.
'Yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kan jami'an tsaro a jihar Katsina. 'yan bindigan sun kai harin ne kan jami'an tsaron da ke hanyar kai daukin gaggawa.
'Yan bindiga sun sace masu ibada 9 a cocin Katolika dake Jihar Benue. Shugaban karamar hukumar Ado LGA da ƴan sanda sun tabbatar da cewa jami'an tsaro sun bi sawu.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun yi aika-aika a jihar Plateau. 'Yan bindigan sun kashe wani mutum daya tare da yin awon gaba da Limami da wasu mutane.
Yan bindiga
Samu kari