Yan bindiga
Yan bindiga sun shiga kauyen Dawaki a kusa da Bwari a Abuja, sun ɗauki mutane da dama amma ƴan sanda sun kai ɗauki kuma ana tsammanin sun ceto mutanen.
Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta samu nasarar rage mugun iri bayan ta hallaka 'yan bindigan da suka addabi jama'a. An kuma kwato makamai a hannunsu.
Rundunar 'yan sanda a jihar Akwa Ibom ta tabbatar da sace basarake, Ogwong A Abang a jihar a daren jiya Asabar 18 ga watan Mayu bayan sun kutsa kai cikin fadarsa.
Gwamnatin Katsina ya koka kan yadda ya ce 'yan bindiga sun sauya salon da suke amfani da shi wajen kai hare-hare a kauyukan jihar, duk da an rage ta'addancin su.
Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina ya bugi kirji kan nasarorin da gwamnatinsa ta samu kan ta'addanci inda ya ce sun rage matsalar da 70% a jihar.
Gwamnonin Arewa maso yamma sun nemi taimakon majalisar dinkin duniya kan magance matsalolin tsaro, talauci, yaran da ba su zuwa makaranta da kiwon lafiya.
Hukumar EFCC za ta binciki dan majalisa, Aminu Sani-Jaji bisa zargin taimakon yan bindiga domin ayyukan ta'addaci a kan cimma manufar siyasa a jihar Zamfara.
Manjo Hamza Al-Mustapha ya koka kan matsalar tsaron Najeriya inda ya ce shugabannin da suka gabata ne suka lalata tsaron kasar da rashin yin katabus.
Rundunar ‘yan sanda a jihar Anambra ta ce ta kaddamar da farautar wadanda suka yi garkuwa da Basil Chukwuemeka, wani babban limamin cocin Katolika a jihar.
Yan bindiga
Samu kari