Yan bindiga
Kwamandan sojin Amurka a Afrika, Janar James Hecker ya ce za su dawo kai farmaki kan Boko Haram da saurann 'yan ta'adda a Afrika domin samar da tsaro.
Wasu da ake zargi da kisan dan majalisar Anambra sun tsere daga hannun ‘yan sanda. Kwamishinan 'yan sanda ya tura jami’ai don kamo su tare da hukunta masu sakaci.
‘Yan bindiga sun kashe wasu matasa biyu a Gwargwada, Abuja, saboda jinkirin fansa. Sun sako wasu mutum uku bayan karɓar N3m. Har yanzu ba a samu gawarwakin ba.
Wasu rahotanni sun ce ana hasashen batan tsohon shugaban karamar hukumar Kalgo a jihar Kebbi, Umar Namashaya Diggi bayan wani mummunan harin yan bindiga.
Hatsabibin dan fashi a jihar Zamfara, Gwaska Dankarami, na shirin mika wuya bayan arangama da Sani Dangote inda wasu suka ce ana nemansa ruwa a jallo.
Gwamnatin jihar Katsina ta yabi sojoji kan nasarar kashe 'yan bindiga 53 da aka kai farmaki maboyar dan bindiga Buzuru da ya shahara da kai hare hare a jihar.
Rundunar sojin Najeriya ta kai farmaki kan wasu 'yan bindiga da suka shahara da kai hare hare a Sabon Birni. Wani da aka ceto ya bayyana yadda maboyar ta ke.
Masu garkuwa da mutane, dauke da muggan makamai sun farmaki gidan wani faston cocin RCCG. An ce 'yan bindigar sun kashe dan faston tare da sace matarsa.
Wasu mahara da ake kyautata zaton fulani makiyaya ne sun kai faraminɗaya bayan ɗaga kan mutanen kauyuka da dama a jihar Benuwai, sun hallaka akalla 19.
Yan bindiga
Samu kari