Yadda Yan Bindiga Suka Sace Mutum 13 Yayin Kazamin Harin Da Suka Kai Wani Kauye A Neja

Yadda Yan Bindiga Suka Sace Mutum 13 Yayin Kazamin Harin Da Suka Kai Wani Kauye A Neja

  • Yan bindiga sun kai hari kauyen Maijaki da ke karamar hukumar a daren ranar Juma'a inda suka sace mutum 13
  • Mai magana da yawun shugaban karamar hukumar Lapai, Abdullahi Umar, ya tabbatar da harin ya kuma ce an jikkata wasu da dama
  • Wni mazaunin garin, Aliyu Gimba, shima ya tabbatar da harin, ya ce maharan sun sace mutane 13, sannan sun harbi wasu

Neja - Yan bindiga sun sace mutane 13 bayan harin da suka kai a kauyen Maijaki a karamar hukumar Lapai ta Jihar Niger.

Da ya ke magana da The Cable a ranar Juma'a, Abdullahi Umar, kakakin shugaban karamar hukumar Lapai, ya tabbatar da lamarin.

Taswirar Jihar Neja.
An Sace Mutane 13 A Yayin Da Yan Bindiga Suka Afka Wani Gari A Neja. Hoto: @TheNationNews.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hakan na zuwa ne bayan yan bindiga sun kai hari babban asibiti na Abdulsalami Abubakar a Gulu, karamar hukumar Lapai sun kashe mutum biyu, sun sace ma'aikatan lafiya.

Umar ya ce harin na baya-bayan ya faru ne a daren ranar Alhamis, ya kara da cewa an tura jami'an tsaro zuwa yankin.

Ya ce:

"Eh, da gaske ne. Ban san takamamen lokacin da aka kai harin ba, amma cikin dare ne."
"An tura jami'an tsaro zuwa unguwar. Akwai jami'an tsaro da unguwanni da ke makwabtaka da dajin Kpashimi ina ake kyautata zaton yan bindigan suka kafa sansani."

Wani mazaunin garin ya tabbatar da harin

Aliyu Gimba, wani mazaunin garin shima ya tabbatar da harin, ya ce maharan sun sace mutane 13, sannan sun harbi wasu.

"Harin ya faru misalin karfe 1 na daren Juma'a. Ya faru da tsakar dare. An raunata mutane da yawa, saboda maharan sunyi harbe-harbe.

"Sun tafi da mutane 13 a nan kauyen Maijaki a Lapai."

An yi kokarin ji ta bakin kakakin yan sandan jihar, Wasiu Abiodun amma bai amsa kira da sakon tes ba.

Yan Bindiga Sun Kai Hari Masallaci A Taraba, Sunyi Kisa, Sun Sace Dan Kasuwa Da Dansa

A wani rahoton, wasu masu garkuwa da mutane kimanin su 10 sun kai hari wani masallaci a Jalingo, babban birnin Jihar Taraba a ranar Alhamis.

Maharan sun kashe mutum daya sun kuma sace wani dan kasuwa da dansa, Daily Trust ta rahoto.

Masu garkuwan sun afka masallacin da ke Jalo Junction ne a unguwar Saminaka na Jalingo da yamma yayin sallar Magariba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel