Babban bankin Najeriya CBN
Emefiele da Tinubu ya dakatar a ranar Juma'a 9 ga watan Yunin da muke ciki, ya yi abubuwa da dama a kujerarsa ta CBN da suka janyo masa suka daga 'yan Najeriya.
Tsohon sanatan Bayelsa ta gabas a majalisar dattawa, Ben Murray-Bruce, ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu na daukar matakan da suka dace a gwamnatinsa.
Za a ji cewa Godwin Emefiele ya ga ta kan shi domin Hukumar DSS ba ta da niyyar fito da shi. Bisa dukkan alamu dakataccen Gwamnan CBN zai kara kwanaki a tsare.
Jam'iyyar Labour ta su Peter Obi ta nemi a kama shugaban hukumar zabe mai zaman kanta INEC tare da binciken abin da ya aikata a zaben shugaban kasa da gabata.
Rahoton da muka tattara ya bayyana yadda gwamnan CBN ya sanya Naira ta sha bakar wahala duk da kasancewarta mai daraja. An kuma fadi tarihon sauran gwamnoni.
Dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, na tsare a hannun jami’an tsaro na farin kaya kamar yadda rundunar yan sandan sirrin ta sanar.
Wani bidiyo ya bayyana a soshiyal midiya na jami'an tsaro kewaye da dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele a wani filin jirgin sama.
Sanata Shehu Sani ya bayyana kadan daga abubuwan da suka faru a lokacin da Emefiele ke kan kujerar gwamnan CBN. Ya ce ta zama wurin cire kudi ga wasu a kasar.
Sowore, dan takarar shugaban kasa a zbaen bana ya bayyana bukatar kama Buhari da wasu manyan kasar nan kan rikicin kudin da ya faru da kuma ma kama Emefiele.
Babban bankin Najeriya CBN
Samu kari