Jihar Borno
Rundunar sojojin saman Najeriya ta samu nasarar hallaka 'yan ta'adda masu yawa a jihar Borno. Sojojin sun yi ruwan wuta kan miyagun a cikin daji.
Kwamishinan kudi na jihar Borno, Ahmed Ali Ahmed ya kwanta dama. An ce ya rasu ne a safiyar yau Litinin, 26 ga Agustan 2024 a cikin gidansa da ke Maiduguri.
'Yan ta'adda masu dauke da makamai sun dade suna tafka ta'asa a Najeriya. 'Yan ta'adda sun hallaka wasu daga cikin manyan sarakuna da ake da su a kasar nan.
Dakarun rundunar sojojin sama sun samu nasarar hallaka manyan kwamandojin 'yan ta'adda a jihar Borno. Sojojin sun kashe su ne a wasu hare-hare ta sama.
A rahoton hukumar NBS na watan Yuli, farashin gas din girki ya sauko da kaso 14.23. An ce ana sayar da gas din kan N5,974.54 a Yuli maimakon N6,966.03 a Yuni.
Gwamnan Farfesa Babagana Umaru Zulum.ya ɗaba tallafin hatsin da jihar Borno ta karɓa daga gwamnatin tarayya, akalla magidanta 10,000 suka amfana a Mafa.
Sojojin Najeriya sun samu nasara kan yan Boko Haram bayan sun fafata yayin wani fada da suka yi a Maiduguri. Sojojin sun samu nasarar kashe Abu Rijab da ake nema.
An fara samun saukin farashin kayan gwari a kasuwannin Arewa maso gabas da suka hada da Borno, Yobe da Adamawa. Yan kasuwa sun fadi dalilin samun saukin.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara kan 'yan ta'addan Boko Haram. Sojojin sun hallaka wani babban kwamandan kungiyar da wasu mutum biyu a wani samame.
Jihar Borno
Samu kari