Arewa
Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya sake mika kasafin naira biliyan 24 don neman amincewar Majalisar yayin da ya himmatu wurin ayyyukan raya kasa a jihar.
Kotun Daukaka Kara ta ce abin da aka gani a takardar da ta fitar na hukuncin shari'ar kuskure ne na wallafa kuma bai karyata sakamakon da kotun ta yanke ba.
Yayin da kotun daukaka kara ta saki takardun CTC, jami'yyar NNPP ta yi martani inda ta ce da nufi kotun ta ki sake takardun da wuri sai yanzu saboda babu gaskiya.
Babban Bankin Duniya (WB) ya yi hasashen cewa akalla 'yan Najeriya miliyan 2.8 ne za su shiga kangin talauci nan da karshen shekarar 2023 zuwa 2024.
Mamba mai wakiltar Pankshin ta Arewa a majalisar dokokin jihar Filato, Gabriel Dawang, a ranar Talata, 21 ga watan Nuwamba, ya zama sabon shugaban majalisar.
Yayin da ake dakon yanke hukuncin shari'ar zaben gwamnan jihar Nasarawa, rundunar 'yan sanda ta girka jami'an tsaro a jihar don dakile ta da zaune tsaye.
Hedikwatar tsaro ta bayyana ainihin yadɗa dakarun sojojin Najeriya suka fatattaƙi yan ta'addan da suka farmaki ayarin motocin Mai Mala Buni ranar Asabar.
Hukumar makarantar Jami'ar Usman Dan Fodio ta karyata jita-jitar cewa 'yan bindiga sun kai hari cikin makarantar tare da hallaka wani mutum daya.
Wasu 'yan bindiga sun sace matar dagaci a kauyen Ruwandorawa da ke jihar Zamfara bayan sun bindige wani dan sanda da kuma sace wasu mutane 15 a kauyen.
Arewa
Samu kari