Abun Bakin Ciki
Mun samu labarin rasuwar mahaifiyar jajirtaccen dan sandan da aka dakatar, DCP Abba Kyari wadda ta rasu a yau Lahadi bayan fama da jinya. Za ayi jana'iza a Borno.
Kungiyar ƙabilar Igbo, Ohanaeze Ndigbo ta musanta jita-jitar cewa ta na shirin zuwa Sokoto domin ba 'yan Arewa hakuri kan juyin mulkin 1966 a Najeriya.
Tsohon karamin Ministan ilimi a Najeriya, Cif Kenneth Gbagi ya riga mu gidan gaskiya, marigayin ya rasu ne a jiya Asabar 4 ga watan Mayu a jihar Delta.
Hadimin Gwamna, Babagana Umara Zulum a bangaren harkokin al'umma, Cif Kester Ogualili a ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da jinya a yau Asabar.
Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi ya sha alwashin sanya hannu a dokar kisan kai ga masu ba 'yan bindiga bayanan sirri wanda suke cutar da al'umma.
Wasu hatsabiban 'yan bindiga sun sake kai mummunan hari a karamar hukumar Birnin Gwari a Kaduna inda suka sace Dagatai biyu da hallaka 'yan banga takwas.
Wata dalibar aji uku a jami’ar kimiyya da fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil, Aisha Yahaya ta rigamu gidan gaskiya. An tsinci gawar wata dalibar a dakinta.
An shiga jimami bayan wasu dalibai guda biyu sun gamu da ajalinsu a hatsarin jirgin ruwa a jihar Kano a hanyarsu ta komawa kwalejin aikin gona ta Audu Bako.
Fitattun mawakan kudancin Najeriya, Davido da Wizkid sun sake kwaɓewa a kafofin sadarwa inda suka yi ta jifan junansu da munanan kalaman batanci.
Abun Bakin Ciki
Samu kari