Abun Al Ajabi
Mai fafutukar kasar Yarbawa, Sunday Igboho ya zargi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da kisan mahaifiyarsa da kanwarsa da kuma neman hallaka shi.
Wani mutum da ya ziyarci shagon siyar da adaidaita ya cika da mamaki bayan an sanar da shi cewa miliyan 2.6 ake siyar da shi a yanzu. Ya daura laifin kan dala.
Wani karamin yaro ya yi fice a soshiyal midiya saboda yanayin dariyar da ya dunga yi yayin da ake susa masa kunne da auduga. Mutane da dama sun yi martani.
Wasu ma’aurata sun koka yayin da bakin da suka gayyata suka ki hallara. Ma’auratan sun kasha fiye da naira miliyan 43 kuma suna sa ran samun baki 88.
Lauyoyin da ke kare jarumar TikTok da ke tsare, Murja Ibrahim Kunya, sun yi barazanar maka gwamnatin Kano a gaban alkali cikin awanni 24 idan ba a bar sun gan ta ba.
Rundunar ‘yan sandan Cross River ta kama wani matashi da ya kashe mahaifiyarsa mai shekaru 62 a Calabar yana mai zarginta da tabarbarewar dukiyarsa.
Shehu Sani ya yi Allah wadai da kiran da Malamin Musulunci ya yi na neman a kasha matar Shugaban kasa Bola Tinubu, Sanata Oluremi Tinubu. Ya ce ba abun yarda bane.
Wata matashiya ta ce ta ziyarci kasuwar kauye a jihar Enugu kuma ta yi nasarar siyan bokiti ghuda na shinkafa kan N3,000, mutane da dama sun nuna shakku a kai.
Shugaban kungiyar Shi'a, Sheikh Ibrahim Zakzaky ya bayyana cewa likitocin da suka duba shi sun cika da mamaki sakamakon cin karo da suka yi da harsasai 38 a kansa.
Abun Al Ajabi
Samu kari