Wata Uwa Mai ‘Ya’ya 22 da ke Son Karin Yara 105 Ta Ba da Labarinta Yayin da Aka Kama Mijinta

Wata Uwa Mai ‘Ya’ya 22 da ke Son Karin Yara 105 Ta Ba da Labarinta Yayin da Aka Kama Mijinta

  • Kristina Ozturk, mutuniyar kasar Rasha mai shekaru 26, ta ba da labarin iyalinta mai yara 22 a wani bidiyon Instagram mai tsuma rai
  • Bata yarda daure miloniyan mijinta da aka yi na shekaru takwas ya hana ta cimma mafarkinta na mallakar yara nata na kanta guda 105 ba
  • An haifi diyarta ta farko, Victoria a aurenta na baya a 2014, yayin da karamin danta, Olivia, ya iso a watan Janairun 2021

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Kristina Ozturk, mai shekaru 26 daga Moscow, ta ba da mamaki a duniya da labarin iyalinta mai ban mamaki.

Ta haifi yaranta guda 20 cikin shekara daya, tana mai godiya ga matan da suka daukar mata cikin. Bidiyonta na Instagram ya nuno kyawawan yaranta suna masu bayyana kansu da ranar haihuwarsu.

Kara karanta wannan

Kamar almara: Matar aure ta datse igiyar aurenta na wata 6, bidiyon ya jawo muhawara

Kristina Ozturk ta mallaki yara 22 a duniya
Uwar ‘Ya’ya 22 Wacce Ke Son Karin Yara 105 Ta Ba da Labarinta Yayin da Aka Kama Mijinta Hoto: @batumi_mama.
Asali: Instagram

Bidiyon ya yadu kuma ya tsuma zukatan miliyoyin jama'a. Kristina, wacce ke auren wani miloniya da aka yankewa zaman gidan maza, ta ce tana mafarkin mallakar babban zuri'a mai yara 105 nata na kanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An haifi babbar diyarta, Victoria, a aurenta na baya a 2014, yayin da karamin danta, Olivia, ya iso a watan Janairun 2021.

Mijin matar da ta haifi yara 44 ya gudu

A wani labarin kuma, mun ji cewa ba tare da samun wadataccen kulawar likita na musamman ba, wata mata mai suna Mama Uganda ta haifi yara 44 a tarayyarta da mijinta.

A cikin wani faifan bidiyo da wani mutum Joe Hattab ya yada a Facebook, matar mai shekaru 40 ta bayyana cewa ita uwa ce mara aure bayan mijinta ya yi watsi da su yayin da ya cika wandonsa da iska da kudadensu.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda wani matashi ya tarwatsa bikin auren tsohuwar budurwarsa ya girgiza intanet

Matar a yanzu haka ita ke daukar dawainiyar yaranta har 38 gaba dayansu - 6 daga cikinsu sun mutu.

Wani Balarabe mai halin kirki ne ya samar musu da gadajen da 'ya'yanta ke kwana akai amma Mama Uganda duk da haka ta samu damar sanya 'ya'yanta duka a makaranta.

Cikin murmushi mai fara'a, matar mai karfin hali ta bayyana cewa likitoci sun gaya mata cewa tana da tsarin haihuwa da akai-akai kuma hakan ya taimaka mata wajen yawan haihuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel