Abun Al Ajabi
Akalla mutane uku ne ake fargabar sun mutu bayan da kasa ta zabtare ta fada kansu a lokacin da suke hakar jar kasa a jihar Nasarawa, har yanzu ba a gansu ba.
An bayyana yadda wata mummunan gobara ta cinye tsohuwa mai shekaru 80 a wani yankin jihar Benue da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya a cikin makon nan.
An samu labarin yadda wata mummunan gobara ta kama tare da yin kaca-kaca da wani katafaren gini a jihar Legas da ke Kudu maso Yammacin Najeriya a yau Lahadi.
Rundunar yan sandan babban birnin tarayya Abuja, sun bayyana rahoton garkuwa da mutane a rukunin gidaje na River Park, Abuja a matsayin kanzon kurege.
Wani dan Najeriya ya bada labari kan yadda kwatsam kwakwalwarsa ta koma fanko a dakin jarrabawa bayan ya kwanta da wata budurwa. Ya kasa rubuta koda kalma daya.
Gwamnatin Akwa Ibom ta yi alkawarin biyan matan da suka haifi 'yan biyu naira dubu 50 duk wata yayin da wadanda suka haifi 'yan uku za su samu naira dubu 100.
Wata matar aure yar Najeriya ta koka bayan ta gano cewa mijinta na da haihuwa tare da wata daban. Watannin dan biyu kuma danginsa sun sani sarai.
Wata matar aure mai juna biyu ta bayyana fargabarta yayin da ranar haihuwanta ya gabato. A cikin bidiyon da ta yada a TikTok tana tunanin yadda za ta haifo dan nata.
Wani tsohon bidiyon attajirin dan kasuwar Najeriya, Femi Otedola a cikin motar haya ya sake bayyana a soshiyal midiya, tare da haddasa cece-kuce cikin jama'a
Abun Al Ajabi
Samu kari