Abun Al Ajabi
Dalibai biyu na kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kogi, Lokoja sun mutu sakamakon shakar hayakin da ke fitowa daga janareta da ke kusa da tagar dakunansu.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa mutane miliyan 88.4 ne suke tafiyar da rayuwarsu cikin matsanancin talauci a Najeriya. Ma'aikatar noma ce ta tabbatar da haka.
Wata kotun majistare da ke yankin Sabo-Yaba a jihar Legas, ta garkame malamin addini Azuka Ohez da matarsa, Mary Ohez kan zargin damfarar kudi miliyan 33.8.
Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa ta kama wani mutum mai shekaru 49, mai suna Muhammad Abubakar dake yaudarar mutane da sunan shi din fatalwa ne.
Shugaban kamfanin Meta, Mark Zuckerberg yanzu ya zama mutum na hudu a jerin attajirai a duniya, inda ya zarce wanda ya kafa Microsoft, wato Bill Gates.
Mata sun fito zanga-zanga a jihar Rivers don nuna damuwa kan kamfanin samar da wutar lantarki na PHED da ke hanasu saduwa da mazajensu saboda zafi.
Wata gobara ta salwantar da rayuwar wani yaro dan shekara 4 mai suna Abubakar Sani, wanda aka fi sani da Musaddiq a Kano. An gano cewa wutar tashi daga kyasta ashana
Wani mai tura baro a kasuwar Kwali dake babban birnin tarayya Abuja ya tsere da buhun shinkafa da wasu kayan wata mata. Za ta aurar da 'diyarta ne.
Wata babbar kotun Kano ta yankewa wata matar aure, Rukayya Abubakar, hukuncin daurin rai da rai kan kishe ‘dan kishiyarta bayan ta jefa shi a cikin rijiya.
Abun Al Ajabi
Samu kari