Abuja
Wani mai kasuwancin siyar da wayoyin hannu a Mararaba jihar Nasarawa, Abdullahi Mohammed ya shaidawa kotu yadda yaro ya sayi babbar waya a wurinsa.
Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, ya bayyana a gaban kotu kan zargin badaƙalar N7.2bn. Sirika ya yi magana kan yiwuwar tafiya gidan kurkuku.
Kudirin karin albashi ga shugaban alkalan Najeriya da sauran ma'aikatan shari'a ya tsallake karatu na biyu a Majalisar Dattawa a yau Alhamis 9 ga watan Mayu.
Shugaban jam'iyyar APC, Dakta Abdullahi Umar Ganduje yace sauyin yanayi da rashin ilimi a tsakanin al'ummar Fulani shi ne babban abin da ya jefa Arewa a matsala.
Yayin da matsalar safarar kwayoyi ta addabi kasar Najeriya, Majalisar Dattawa ta amince da dokar hukuncin kisa kan masu mu'amala da siyar da kwayoyi .
Majalisar wakilai ta fara gudanar da bincike kan kwangilar aikin gina babban titin da ya taso daga Legas zuwa Calabar. Majalisar na zargin akwai lauje cikin nadi.
Kungiyar matasan Arewa ta NEYGA ta bukaci Sanata Ali Ndume ya msyar da hankali kan abin da ya kai shi majalisa ba ya tsaya yana wasu kananan kalamai ba.
Hedikwatar tsaro ta karbi sababbin motocin yaki masu sulke guda 20 daga hannun ma'aikatar tsaro. Ana sa ran motocin za su kara taimakawa wajen yaki da ta'addanci.
Gwamnatin tarayya ta bakin ministan ayyuka David Umahi ta ce zuwa nan da karshen shekarar 2025 za ta kammala aikin gina titin Abuja-Kaduna-Kano-Katsina.
Abuja
Samu kari