Abuja
Babban Bankin Najeriya, CBN ya fitar da sabuwar sanarwa kan asusun bankunan da ba su da lambobin BVN da NIN inda ya ce za a kulle su a farkon shekarar 2024.
Majalisar Dattawa ta bukaci Shugaba Tinubu da ya dakatar da tura kudaden kananan hukumomin da babu zababbun shugabanni a jihohi 16 da ke fadin kasar.
Zaben sabbin shugabanni na kungiyar daliban Najeriya ta kasa ya zama tashin hankali yayin da aka jiyo karar harbe-harbe a kusa da wajen zaben a Abuja.
Fitaccen dan siyasa kuma tsohon kwamishina, Alhaji Shehu Othman ya riga mu gidan gaskiya yana da shekara 91. Iyalansa sun tabbatar da rasuwarsa a ranar Laraba.
Masu garkuwa da mutane sun nemi naira miliyan 16 daga iyalan mata takwas da suka yi garkuwa da su a wani kauyen Abuja. Akwai matar sarkin garin cikin matan.
Hukumar EFCC ta sake bijiro da wata tuhuma kan tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele kan ba da kwangiloli ba bisa ka'ida ba.
Kotun daukaka kara ta sake kwace kujerar dan Majalisar jihar Plateau guda daya tilo da ya rage a jami'yyar PDP inda ta bai wa Farfesa Theodore Bala Maiyaki nasara.
Rundunar 'yan sanda ta ce ta samu nasarar kama wani dan takarar gwamna da wasu mutane uku kan zargin satar sama da naira miliyan 607 daga manhajar Patricia.
Hukumar jarrabawa ta JAMB ta fitar da sabuwar sanarwar ranar rubuta jarabawar UTME na shekarar 2024 inda ta ce za a gudanar a ranar 19 zuwa 29 ga watan Afrilu.
Abuja
Samu kari