Majalisar dokokin tarayya
Benjamin Okezie Kalu ya ce bai da alakar siyasa kai-tsaye da Nkeiruka Onyejeocha da za su yi fada. Wadannan manyan ‘yan siyasa sun fito daga jihar Abia.
Majalisar dattawa ta kare matsayar da aka cimmawa ta siyo motocin alfarma ga ƴan majalisun tarayya duk kuwa da halin matsin tattalin arziƙin da ake ciki a ƙasa.
Majalisar Wakilai ta umarci gwamnan CBN, Yemi Cardoso da ya hallara a gabanta don yin bayani gamsasshe kan matakin daya dauka na cire takunkumin dala.
Ma'aikatan majalisa sun lashi takobin garƙame majalisar tarayya NASS da sauran majalisun dokokin jihohi daga ranar Laraba har sai an cika musu buƙatarsu.
Tsohon shugaban ma su rinjaye a majalisar Tarayya, Alhassan Ado Doguwa ya yi nasara kan abokin takararsa na jam'iyyar NNPP, Salisu Yusha'u a kotun zabe.
Kusan yadda fadar shugaban kasa ta dama, haka aka sha wannan karo a majalisun tarayya. Da wahala Bola Tinubu ya kawo wata bukata, majalisa ta taka masa burki.
Kotun daukaka kara da ke Abuja ta soke nasarar Sanata mai wakiltar Filato ta Arewa, Simon Mwadkwon. An kuma kori dan Majalisar Wakilai na PDP, Musa Avia.
Ikenga Imo Ugochinyere, ya caccaki Sheikh Ahmad Mahmud Gumi bisa kalama. da ya yi na ƙiyayya kan Wike, ya ce bai kamata a naɗe hannu a bar abun ya wuce ba.
Majalisar Wakilan tarayya ta bayyana cewa ya kamata Najeriya ta ayyana dokar ta ɓacu a fannin ilimi idan har ana son inganta harkar koyo da koyarwa.
Majalisar dokokin tarayya
Samu kari