Ado Doguwa Ya Yi Nasara Kan Yaron Kwankwaso, Yusha’u a Kotun Zaben Majalisar Tarayya

Ado Doguwa Ya Yi Nasara Kan Yaron Kwankwaso, Yusha’u a Kotun Zaben Majalisar Tarayya

  • Alhassan Ado Doguwa ya yi nasara a kotun sauraran kararrakin zabe wanda ake ci gaba da shari’a
  • Alhassan ya yi nasara ne kan dan takara a jam’iyyar NNPP, Salisu Abdullahi Yusha’u a mazabar Doguwa/Tudunwada
  • Yayin yanke hukunci, Mai Shari’a, L. Owolabi ya yi fatali da karar dan jam’iyyar NNPP saboda rashin hujjoji

Jihar Kano – Tsohon shugaban ma su rinjaye a majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa ya yi nasara kan abokin hamayyarsa, Salisu Abdullahi Yusha’u.

Doguwa wanda dan jam’iyyar APC ne ya yi nasarar ce kan dan jam’iyyar NNPP a mazabar Doguwa/Tudunwada a jihar Kano, Tribune ta tattaro.

Kotun ta bai wa Ado Doguwa nasara kan dan jam'iyyar NNPP a Kano
Ado Doguwa Ya Yi Nasara a Kotun Zabe. Hoto: Alhassan Ado Doguwa.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotu ta yanke kan Doguwa?

Da ya ke yanke hukuncin a yau Litinin 23 ga watan Oktoba, Mai Sahri’a L.B Owolabi ya ce mai karar ya gaza kawo kwararan hujjoji, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Bazoum: Shugaban Nijar da Aka Hamɓarar Ya Yi Yunkurin Tserewa Daga Hannun Sojoji, Bayanai Sun Fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce rashin kwararan hujjojin tabbatar da abin da ya ke fada shi yasa aka yi fatali da korafin nashi.

Ya kara da cewa daga cikin korafin Yusa’u akwai zargin Doguwa da cin hanci da rashawa da rashin bin dokar zabe, cewar Vanguard.

A kan meye ake karan Doguwa?

Sauran sun hada da rashin samun halastattun kuri’u da za su ba shi damar cin zabe wanda ba su da tushe da za yi amfani da su wurin soke zaben.

Har ila yau, kan maganar ta da tarzoma, duk shaidu 21 sun tabbatar da cewa babu wata tarzoma da dan majalisar ya tayar yayin zaben da aka gudanar.

Kotun ta tabbatar da cewa dukkan shaidu 32 da mai kara ya kawo ba su ba da kwararan hujjoji da za su iya ruguza zaben ba.

Kara karanta wannan

Za Su Kashe Ni – Abokin Fadan Kwankwaso a NNPP Ya Ce Ya Na Fuskantar Barazana

Kotu ta dage sauraran karar da ake kan Doguwa

A wani labarin, babbar kotun Tarayya da ke Abuja ta dage sauraran karar da aka shigar kan dan majalisa Alhassan Ado Doguwa kan zargin kisan kai.

Gwamnatin jihar Kano ta shigar da kara kan zargin ta da tarzoma da kisan kai yayin zaben da aka gudanar a watan Faburairu.

Kotun ta dage karar ce don bai wa gwamnatin jihar damar yin nazari kan rahoton 'yan sanda na kisan kai da aka yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel