Yan ta'adda
Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai hare-haren ta'addanci a wasu kauyukan karamar hukumar Shiroro cikin jihar Neja. Sun hallaka mutum bakwai har lahira.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu da ake zargin 'yan ta'addan Boko Haram ne sun hallaka mutum uku bayan sun tare motarsu a kan hanya a jihar Yobe.
Hatsabibin ɗan ta'adda, Bello Turji ya fitar da wani sabon faifan bidiyo da ya ke ƙaryata hukumomin Nijar cewa sun cafke mayakinsa, Baleri inda ya nuna shi a bidiyo.
Rundunar sojin Najeriya ta yi martani ga 'yan ta'addan IPOB kan cewa ta kashe fararen hula 'yan kabilar Ibo a kudu maso gabas. Simon Ekpa ne ya yi zargin.
Wasu ƴan bindiga sun kai hari fadan sarkin Ninzo a karamar hukumar Sanga da ke jihar Kaduna inda suka yi awon gaba da matarsa a cikin daren jiya Laraba.
Gwamnatin jihar Yobe ta kare matakin amfani da tubabbun 'yan Boko Haram wajen samar da tsaro. Gwamnatin ta ce suna taimakawa wajen yaki da ta'addanci.
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta cafke wasu manyan mutane da suka hada da dan majalisar dokokin jihar, da wani hakimi da ke da alaka da ‘yan fashi a jihar.
Gwamnatin jihar Niger ta dora laifin gaza ceto wadanda suka makale a karkashin mahakar ma'adanai kan rashin tsaro da ya addabi yankin Galadima-Kogo.
Dakarun rundunar sojojin hadin gwiwa ta kasa da kasa (MNJTF) sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda 140 yayin gudanar da ayyukansu a yankin tafkin Chadi.
Yan ta'adda
Samu kari