Mafi karancin albashi
Kungiyar yan kasuwa TUC ta yi karin haske kan karin kaso ashirin da biyar cikin dari da kaso talatin da biyar da gwamnatin tarayya ta ce ta yi wa ma'aikata.
Kungiyoyin kwadago na NLC ds TUC sun ba gwamnatin tarayya sabon wa'adi kan aiwatar da tsarin sabon mafi karancin albashi a kasar nan. Sun yi barazanar yajin aiki.
Wasu daga cikin gwamnonin Najeriya, sun yi wa ma'aikatan gwamnati a jihohinsu karin albashi, saboda tsadar rayuwa da ake fama da ita a kasar nan.
Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru ya sanar da yin karin N10,000 ga albashin ma'aikatan jihar. Wannan shi ne karo na biyu da gwamnan yake kara albashi.
Gwamna Bassey Otu na jihar Kuros Riba ya amince da biyan sabon mafi karancin albashi N40,000 ga ma'aikatan jihar yayin bikin ranar ma'aikata a Najeriya.
Gwamnati ta ayyana ranar 1 ga Mayu, 2024 a matsayin rnar da sabon albashin ma'aikata zai fara aiki. Shugaba Tinubu ya yaba da gudunmawar da ma’aikata ke bayarwa.
Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta yi fatali da matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na yi wa ma'aikata karin albashi. Ta ce bata lokaci ne kawai.
Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ta amince da yi wa ma'aikata da 'yan fansho karin albashi. Zai fara aiki daga Janairun 2024.
Gwamna Godwin Obaseki ya sanar da N70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan jihar Edo kuma ya ce zai fara aiki a farkon watan Mayu, 2024.
Mafi karancin albashi
Samu kari